Daga Hauwa’u Maikuɗi Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe jami’an ’yan sanda biyar, tare da jikkata wasu biyar, bayan k...
Daga Hauwa’u Maikuɗi
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe jami’an ’yan sanda biyar, tare da jikkata wasu biyar, bayan kai musu harin kwanton ɓauna a kan hanyar Gusau zuwa Sakkwato, a Jihar Zamfara.
Harin ya faru ne a ranar Litinin, 2 ga Nuwamba, 2026, a tsakanin yankin Gidan Kano da Kwanar Sado, da ke Ƙaramar Hukumar Maradun ta jihar.
Bayanan da TNL Hausa ta samu sun nuna cewa jami’an ’yan sandan suna cikin wata motar sufuri ta gwamnatin jihar, wadda aka fi sani da Bazamfara, a lokacin da lamarin ya faru.
Tawagar jami’an na kan hanyarsu ne daga Sakkwato zuwa Gusau domin samar da tsaro yayin zaɓen fid da gwani na jam’iyyar APC na kujerar Sanatan Zamfara ta Arewa, wanda aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda.
Wani jami’in ’yan sanda da ya tsira daga harin ya shaida wa jaridar PUNCH cewa, tawagarsu tana tafiya ne cikin motoci uku, lokacin da maharan suka buɗe wa motar da ke bayansu wuta.
Sai dai mai magana da yawun rundunar ’yan sanda ta shiyya ta 10 da ke Sakkwato, DSP Abdullahi Faruk Ambursa, ya tabbatar da mutuwar jami’ai biyar da kuma jikkatar wasu biyar.
Ya ce an ajiye gawarwakin mamatan a ɗakin ajiyar gawa na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sakkwato, inda ya ƙara da cewa ba za a bayyana sunayensu ba sai an sanar da iyalansu a hukumance.
A wani rahoto da jaridar Leadership ta wallafa, an bayyana cewa rundunar ’yan sanda ta fara gudanar da bincike domin gano waɗanda suka kai harin da kuma cafke su.
Haka kuma, wasu majiyoyi sun yi iƙirarin cewa akwai jami’an da har yanzu ba a san halin da suke ciki ba, sai dai rundunar ba ta tabbatar da wannan batu a hukumance ba.
Harin na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar tsaro ke ci gaba da addabar wasu sassan Arewa maso Yammacin Najeriya, lamarin da ke janyo asarar rayuka da jikkata jami’an tsaro da fararen hula.

No comments