Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Ana Duba Yiwuwar Maye Gurbin HND Da Digiri A Kwalejojin Fasaha

Daga Hadi Bawa A ranar Talata ne shugabanni da masu ruwa da tsaki na Kwalejin Kimiyya da Fasaha da sauran cibiyoyin bayar da tak...

Daga Hadi Bawa

A ranar Talata ne shugabanni da masu ruwa da tsaki na Kwalejin Kimiyya da Fasaha da sauran cibiyoyin bayar da takardar shaida suka fara muhawara kan kudirin maye gurbin HND da Digiri.

 A cikin wata wasika mai dauke da sa hannun Daraktan ma’aikata na hukumar kula da ilimin fasaha ta kasa, Lawal Hafiz ya aika wa dukkan shugabanni Kwalejojin Kimiyya da Fasaha a fadin kasar nan ta ce, taron zai kuma bai wa mambobin damar sake sabunta kira ga Gwamnatin Tarayya, kamar yadda jaridar PUNCH ta ruwaito.

A baya dai gwamnati ta amince da kudurin dokar da ya cire fifiko tsakanin Digiri na farko da HND, amma har yanzu ana jan ƙafa kan fara aiwatar da tsarin.

Kudirin dokar dai na neman cire wa daliban da suka kammala karatun kimiyyar kere-kere daga takwarorinsu na jami’o’i guraben aikin yi da karin girma a wuraren aiki ba tare da la'akari da tsarin da ake a kai a baya ba.

Kudirin ya kuma nemi kawo ƙarshen wariyar da masu ruwa da tsaki a jam'io'i ke nuna wa na makarantun Kimiyya da Fasah, wanda aka dade suna kokawa a kansa.

Ƙudurin dokar da Sanata Ayo Akinyelure ya gabatar a gaban majalisa, an yi mata karatu na uku a zauren majalisar Dattawa a zauren majalisar Tarayya.

Da yake magana a kan Æ™udurin dokar, tsohon Ministan ilimi, kuma wanda ya jagoranci kwamitin duba dokar a gaban majalisa, Malam Ibrahim Shekarau (APC, Kano ta tsakiya) ya ce, “Samar da dokar da za ta soke tare da haramta nuna wariya a tsakanin masu Digiri na farko da kuma babbar difloma ta Æ™asa da nufin daukar ma’aikata aiki a Nijeriya ba zai yiwu ba. Ya ce ma'aikatu suna shakkar kwarewar masu HND idan aka kwatanta su da takwarorinsu na sauran manyan makarantu a Nijeriya."

Wasikar ta NBTE a wani bangare tana cewa, “Na rubuto ne domin in gayyace ku zuwa taron tattaunawa na kasa ta kwana daya kan makomar shirin HND a tsarin koyarwa a Nijeriya.

"Manufar tattaunawar ita ce duba batutuwan da suka shafi ci gaba da nuna wariya da ake nunawa masu takardar shaidar difloma ta kasa da kuma fitar da hanyoyin magance matsalar da ta dade tana ci wa tsarin ilimi tuwo a kwarya.

 “Muna fatan tattaunawar za ta duba Æ™udurin maye gurbin shirin HND da Bachelors of Technology (B.Tech);  da kuma ko sabunta kira ga shugaban Æ™asa ya amince da Æ™udurin dokar da Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta zartar na 'Dokar Kawar da hana wariya da nuna bambanci tsakanin Digiri na farko da Babbar Diploma ta kasa a cikin wannan Sana'a don manufar aiki da kuma  bubuwan da kuma magance matsalar," in ji sanarwar.

No comments