Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Gwamnatin Zamfara Ta Yi Watsi Da Zargin Ware Naira Biliyan 19.3 Don Siyen Kayan Kicin

Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi watsi da zargin da aka yi mata na cewa ta ware Naira Biliyan 19.3 don sayen kayan kicin a shekarar...

Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi watsi da zargin da aka yi mata na cewa ta ware Naira Biliyan 19.3 don sayen kayan kicin a shekarar 2024, inda ta bayyana cewa ana yaÉ—a waÉ—annan Æ™arairayi ne don a kautar da hankalin jama'a. 

A ranar Talata ne wata kafar sadarwa ta wallafa cewa kasafin kuÉ—in jihar Zamfara ya ware Naira Biliyan 19.3 wajen sayen kayan kicin da na wurin cin abinci a cikin kasafin kuÉ—in shekarar 2014.

Cikin martanin da ya mayar kan wannan zargi, a wani taron manema labarai da ya gabatar a Gusau, Kwamishinan kasafi da tsare-tsare, Mallam Abdulmalik Gajam ya nuna takaicin sa game da wannan Æ™agaggen rahoto. 

Mallam Gajam bai tsaya nan ba, sai da ya fayyace dalla-dalla yadda gaskiyar abin ke game da waÉ—annan kuÉ—aÉ—e Naira Biliyan 19.3, da aka ware ma wasu ayyuka a mai'aikatar ilimi. “Wannan kafar sadarwa da ta yaÉ—a wannan labari, sai ta tsakuro wani É“angare na kasafin, ta kau da kai ga muhimman fannonin da cikakken kasafin ya Æ™unsa."

Gajam ya ci gaba da cewa, “Tsarin yadda aka kasafta Naira Biliyan 19.3 a Æ™arÆ™ashin ma'aikatar ilimi yana nan a layin manyan ayyuka.

"Sunan da ke ciki na Wurin Cin Binci da Kicin, yana Æ™unshe ne cikin rukunin wasu ayyuka, waÉ—anda suka haÉ—a da shirin nan na AGILE, gina makarantun Firamare na yanki, samar da makarantar Firamare ta musamman a Gusau, sawo kayan aikin kicin da na dafa abinci ga duk makarantun gwamnati a kan Naira Miliyan 40, gina cibiyar horar da Malamai, da Æ™irÆ™iro da shirin asusun ci gaban Malamai. 

"Duk waÉ—annan ne suka haÉ—u suka tara Naira Biliyan 19.3. 

Kwamishinan ya kuma yi ƙarin haske da cewa, gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta zo ne domin ta rage ɓarnatar da dukiyar Baitulmali, tare da rufe duk wasu hanyoyin sata. "Ba za a taɓa samun mu cikin irin wannan rashin iya aiki da aikin banza ba."

No comments