Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da rabon takin zamani da sauran muhimman kayan noma domin tallafa wa manoma a ka...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da rabon takin zamani da sauran muhimman kayan noma domin tallafa wa manoma a kakar noman rani a faɗin jihar.
An Ć™addamar da shirin ne a ranar Alhamis a cibiyar Fadama III da ke Ć™arĆ™ashin Ma’aikatar Noma ta jihar a Gusau.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, kayayyakin da aka raba suna da matuƙar muhimmanci wajen ƙara yawan amfanin gona, rage asarar da ake yi bayan girbi, da kuma bunƙasa noma mai ɗorewa.
Kayayyakin da aka raba sun haɗa da buhunan takin NPK 3,920, buhunan takin Urea 1,956, litar maganin kashe ciyawa 3,920, litar maganin kashe ƙwari 1,956, da kuma fakitin maganin shafa iri 3,920.
An tsara rabon ne domin kaiwa ga manoma a sassa daban-daban na jihar, musamman ƙananan manoma da ke dogaro da noma a matsayin hanyar samun abinci da kuɗin shiga.
A jawabinsa, Gwamna Lawal ya jaddada cewa shirin na daga cikin matakan da gwamnatinsa ke É—auka domin Ć™ara yawan noma, inganta tsaron abinci da kuma bunĆ™asa rayuwar al’umma.
Ya ce noma shi ne ginshiƙin tattalin arzikin jihar, don haka wajibi ne gwamnati ta samar wa manoma kayan aikin da za su taimaka musu su yi noma cikin inganci.
Ya bayyana cewa shirye-shiryen NG-CARES sun samar da tubalin da ya bai wa gwamnatin jihar damar cimma nasarori a bangaren noma, musamman ta hanyar tallafa wa dubban ƙananan manoma da iri masu inganci, magungunan gona da shawarwarin dabarun noma.
Gwamnan ya yi kira ga manoman Zamfara da su yi amfani da kayayyakin da aka ba su yadda ya kamata, domin cimma manufar bunƙasa noma mai ɗorewa.
Ya ƙara da cewa, gwamnatinsa za ta ci gaba da amfani da irin waɗannan shirye-shirye wajen ƙara samar da abinci a cikin gida da rage dogaro da shigo da kayayyakin abinci daga ƙasashen waje.
Dangane da matsalolin tsaro, Gwamna Lawal ya amince cewa ƙalubalen tsaro na daga cikin manyan matsalolin da ke addabar noma a halin yanzu. Ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da ƙarfafa tsarin tsaro a yankunan karkara domin manoma su samu damar komawa gonakinsu cikin kwanciyar hankali.
Haka kuma, ya yaba da goyon bayan da Gwamnatin Tarayya da abokan hulÉ—a na ci gaba ke bayarwa wajen aiwatar da shirin NG-CARES, yana mai cewa haÉ—in gwiwa tsakanin bangarori ne kaÉ—ai zai tabbatar da nasarar manufofin ci gaban noma da tattalin arziki a jihar.
No comments