Daga Haidar Aliyu A goman ƙarshe na watan Ramadan da ta gabata, na samu gayyata daga abokin aikinmu Muhammad Ɗanjuma Katsina, m...
Daga Haidar Aliyu
A goman ƙarshe na watan Ramadan da ta gabata, na samu gayyata daga abokin aikinmu Muhammad Ɗanjuma Katsina, mawallafin jaridun Katsina Times da Katsina City News. Ya gayyace mu Sallah da sada zumunta.
Zuwanmu na Sallah, ni da wasu abokan arziƙin da ya gayyata daga wasu jihohi, ya ba mu damar yawan gani da ido a jihar Katsina, tare da tambaya a kan wasu yankuna na Katsina.
Abin da muka gani a ƙasa ya ba mu mamaki, wanda har na fara tambayar ko akwai Gwamnan da ya kai na Katsina aikin raya ƙasa a ƙasar nan? Wannan bincike ne kawai zai tabbatar da hakan. Amma abin da muka gani yana da girgiza zuciya.
Daga Kaduna mun bi ta garin Funtua domin sada wani zumunci. Mun ga wani irin aikin faɗaɗa hanya da ake yi a birnin Funtua mai tarihin shahararrun mutane.
An faɗa mana aikin dam na garin Ɗanja da ake yi, wanda har muka leƙa muka ga yadda ake aikin, wanda baki ɗayansa zai canza tsarin fasalin tattalin arziƙin mutanen yankin.
A garin Kafin Soli, aka nuna mana wani aikin ruwa, wanda ina iya kiran sa babban aikin ruwa da ban taɓa jin kamarsa a yankin nan ba.
Mun ga filin da ake shirin wani aiki da ake kira “mai da birane gonaki,” wani aiki da ya kawo cece-kuce a kansa.
An ce aiki ne tsakanin wani kamfani da Gwamnatin Tarayya, wanda dole sai gwamnatin jiha ta shiga wasu wurare kamar ba da filin da za a yi aikin da kuma ba bankuna tabbacin cewa da sanin gwamnatin jiha ake aikin.
A bakin shiga garin Ɗandagoro, wanda daga nan sai birnin Katsina, mun ga wata hanya sabuwa da aka yi. Aka ce ta taso ne daga wani gari mai suna Ɓatagarawa ta haɗe har garin Shinkafi. An ce ana kiran ta sabuwar ganuwar Katsina, wani tsari na buɗa gari da faɗaɗa shi.
Mun ga wajen wani katafaren haɗa taraktocin noma. An ce daga jihar Neja aka ɗauko tsarin. An faɗa mana wani tsari ne wanda za a wadata manoma da taraktoci da yawa.
Abin da muka gani kan hanya ya sanya, bayan kwana ɗaya da isar mu Katsina, muka yanke hukuncin shiga garin mu ga me aka yi wa jihar.
Mun tarar da wani aikin hanyoyi mai kyau da ɗaukar hankali, wanda Abuja kaɗai ke da irin sa a ƙasar nan.
To, tsari ne daga duk inda ka shiga birnin za ka kai kanka tsakiyar birnin ba tare da tambaya ba, a bisa tagwayen hanyoyi.
Daga hanyar Daura har zuwa tsakiyar birnin Katsina kusa da masallacin Juma’a da gidan sarki, tagwayen hanyoyi ne.
Daga hanyar Mani zuwa unguwar 'Yan Boko ta Lokost zuwa Ƙofar Marusa zuwa masallacin Juma’a da gidan Sarki, kana kan tagwayen hanyoyi ne.
Daga Kofar Guga zuwa tsohuwar kasuwa har Ƙofar gidan Sarki, kana kan tagwayen hanyoyi ne.
Mun tarar ana aikin tagwayen hanyoyin da ya taso daga Shinkafi har zuwa masallacin Juma’a da gidan Sarki.
Da kuma daga titin IBB, wanda zai kama daga Kano idan ka shigo Katsina, ana aikin tagwayen hanyoyin har zuwa babban masallacin Juma’a.
Mun tarar da hanyoyin kamar yaƙi, ba tsagaita wuta, ana ta rusau da gina hanyoyin ruwa.
An faɗa mana an fara biyan diyya na aikin titin Ƙofar 'Yandaka zuwa gidan Sarki.
Mun ga yadda aka sanya alama a gidajen da za a rusa idan aikin ya taso.
An faɗa mana aikin zai kai har ga titin daga Mobil zuwa Rafin Daɗi.
Tsarin shiga gari daga kowace kusurwa har tsakiyar gari a kan tagwayen hanyoyi -duk ƙasar nan ban san jihar da take da wannan ba, amma ƙila akwai?
A mujallar Katsina City News da nake karantawa a otel ɗin da aka sauke mu, na karanta yadda aka biya kuɗin sallamar ma’aikata sama da Naira biliyan ashirin! Wawooo, biliyan ashirin?
Na karanta yadda aka ɗauki malaman makaranta sama da dubu biyar da ma’aikatan lafiya sama da dubu biyu.
A kusa da ofishin Katsina Times da ke Ƙofar Ƙaura, na ga an rubuta a ƙofar wani shago da sunan “Kantin Sauƙi,” wanda aka ce ana ba ma’aikatan gwamnati bashin abinci a bisa wani tsari a cire cikin albashinsu a ƙarshen wata, ana kuma yi masu wani rangwame na musamman.
Mun je asibitin ƙashi da ake kira Amadi Rimi da ke garin Ɓatagarawa, inda aka kammala ginin wani sashe na masu cutar ƙoda wanda babu irin sa a duk ƙasar nan (Dialysis Centre), da yadda ake ƙoƙarin mai da asibitin ya zama wurin neman lafiya ga 'yan Nijeriya da maƙwabta.
BABBAR CIKAS DA MUKA GANI
Katsina Cibiyar Iiimi ce a tarihin duniya tun zamanin dauri. Ɗakin karatun jihar shi ne mafi koma baya a duk ƙasar nan. Tun tsohon ginin ne, wanda aka yi domin karamar hukumar Katsina, shi ne har yanzu yake zama a matsayin ɗakin karatun jihar.
Zamani ya zo da ɗakin karatu ya zama cibiyar ayyuka daban-daban, kuma yanzu ƙasashen duniya suna ta haɓaka cibiyoyin karatunsu.
Amma Katsina an bar ta a baya. An faɗa mana akwai lokacin da sashen ilimi na ƙasar Amurka da Ingila ya so ya buɗe wani sashe a ɗakin. Har sun turo ƙwararru, sai suka soke zancen. Aka ce sai dai suka je National Library da ke Katsina suka buɗe.
An ce ƙasar Jamus ma ta so buɗe wani sashe na musayar al’adu, shi ma ginin ya sanya suka fasa.
An ce tsohuwar gwamnatin Masari ta yi yunƙurin gina wani, amma maganar ta lalace wannan gwamnatin ta hau.
CIKAS NA BIYU DAGA GWAMNATIN TARAYYA
Wani abu da muka gani shi ne manyan hanyoyin da suka haɗa Katsina da jihohin Kano da Kaduna duk sun lalace -sun mutu. Azaba masu motoci ke sha a kansu.
Daga Kano zuwa Katsina aikin ya tsaya ba dalili. Ita ce hanyar da ta haɗa garin da duk wata hulɗar kasuwanci da ke wasu jahohi.
Hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Katsina ita ma ta mutu, aikin yana tafiyar hawainiya.
Titin Katsina zuwa Sakkwato ta Funtua ita ma ta mutu.
Hanyar Katsina zuwa Daura ita ma fara mutuwa, babu gyara.
Hanyoyin Gwamnatin Tarayya da suka yi wa jihar zobe duk ba su da kyau.
RA’AYIN MUTANEN GARI
Ana biyan albashi, ana biyan kuɗin sallamar ma'aikata. Ana aiki. ana gani-ga mutumin gari baya da wata matsala da gwamnatin Dikko Radda, in ban da maganar tsaro, wanda mafi nauyinsa yana kan Gwamnatin Tarayya.
Wani mutum da ke kasuwanci a bakin ƙofar tashar Katsina ya faɗa mana cewa, matsalar Dikko Raɗɗa ta Tinubu ce.
Ya ƙara da cewa duk wahalar rayuwa da ake ciki sakamakon tsadar mai ce, wanda Dikko bai da hannu.
"Matsalae tsaro da muke fama da ita, irin rawar da gwamnatin jiha takeiiya takawa, sauran na Gwamnatin Tarayya ne.
“Ka ga mu, in ka ga wani laifin da aka goga wa Dikko, to aikin Tinubu ne”, in ji shi.
No comments