Injiniya Samaila Ma'azu Bawa Dan Majilisasa Ma iwakiltar Karamar Hukumar Faskari a Majilisar dokoko ta Jihar Katsina Daga Aw...
Injiniya Samaila Ma'azu Bawa Dan Majilisasa Ma iwakiltar Karamar Hukumar Faskari a Majilisar dokoko ta Jihar Katsina
Daga Awwal Jibril 'Yankara
A Ranar Lahadi, 31 ga watan Disamba 2023, Matasa masu amfani da kafafen sadarwar zamani na karamar hukumar Faskari, Jihar Katsina.
Suka gudanar da taron sada zumunci na kafa-da-kafa, a cikin garin Faskari, inda a suka karrama wasu daga cikin fitattun dake taimakawa wajen ci gaban karamar hukumar Ta Faskari, Jihar Katsina
Danmajalisa Mai Wakiltar Karamar Hukumar Faskari Injiniya Samaila Ma'azu Bawa Faskari.
Ya yi kira ga Masu san karama mutane yakamata surinka tsaya su natsu suga Mai Mutum Yayi wa Al-Umma ba kawai daga Yasami Wata Kujera ba, a'a a tsaya a natsu a ga wace gudumuwa ya bayar.
Shi ma a na sa jawabin Shugaban karamar Hukumar Faskari Hon Musa Bala Ado kira ya yi ga Matasan Da suguji bayar da Labarin da basujiba ba Sugani ba, Sabo da irin Wadannan Labaran Na Maida Karamar Hukumar ta Faskari Baya.
Mun Sani muna cikin Matsalar Tsaro amman wasu na Kambama Lamafin feye da yadda yake.
Shi ma Malam Ibrahim Musa kira yayi da Matasan suji Tsoran Allah Duk abin da karubuta sai antambaye ka a kan sa Inji Shi.
A ciki Waddan da aka karrama har da babban likitan dake zuwa duba marasa lafiya da kuma tiyata, a babbar asibitin garin na Faskari, Dr. Yakub Salihu Funtua,
Iljiniya Samaila Ma'azu Bawa Dan Majilisa Mai Wakiltar Karamar Hukumar Faskari a Mahilisar Dokoki ta Jihar Katsina, Hon. Musa Bala Ado Shugaban karamar Hukumar Faskari, Hon. Jamilu Muhammad Lion Da Majilisar wakilai ta Abuja Mai wakiltar Kananan Hukomomin Kankara,Faskari Da Sabuwa, Injiniya Aminu Umar Saidu Hakimin Faskari, Alh. Sani Idiris Sambo Hakimin Mairuwa, Hon. Hamza Suleman Kwamishinan Ruwa na Jihar Katsina, Sauran sun hada da Alh.Usaini Na Umma Jagaban Faskari,Injiniua Aminu Barau Mairua,Injiniya Shehu Sallau 'Yankara Barayan Faskari,Alh. Ahmad Musa Wafa Danmalikin Faskari,Injiniya Murtala Sheme Da Sauran su
Anyaba wa Likitan ne, bisa yadda duk runtsi ba ya kauracewa zuwa aikinsa a Faskari, da kuma yadda yake gudanar da aikin cikin girma da arziki tare da mutuntawa, gami da sadaukar da kai.
Shugaban karamar hukumar Faskari Hon Musa Ado ne, ya mika wa likitan shedar yabon, a madadin Matasa masu amfani da kafafen zamani na karamar hukumar Faskari
Kowanne daya da aka karrama Sai da aka fadi irin Alkhairin sa da ya kawo ma karamar Hukumar ta Faskari
A gurin taro Masana ne da dama sukai Bayani da Nasihohi akan ta'amuli da kafar Sada zumunta a ciki harda M.Ashiru Labbo :Yankara, M.Ibrahim Musa Liman Faskari, Da M.Abdulshahid Mahmud Inuwa da dai Sauran su.
No comments