Daga Abdullahi Sambo Richifa, Kano Alhaji Sani Lawan Kofar Mata, tsohon Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano...
Daga Abdullahi Sambo Richifa, Kano
Alhaji Sani Lawan Kofar Mata, tsohon Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, ya rasu.
Marigayin ya kasance fitaccen Jami,in harkokin aikin Hajji, inda ya taba jagorantar Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano. Haka kuma, ya kasance mai taka rawa a harkokin siyasa da al’amuran jama’a a jihar.
Bayanan tarihi Wanda Jaridan National lens ta Samu sun nuna cewa Sani Kofar Mata ya rike matsayin Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kano a lokacin mulkin tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau.
Daga bisani, ya fice daga jam’iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP), inda ya koma Action Congress of Nigeria (ACN) a shekarar 2011 tare da tsohon Mataimakin Gwamnan Kano, Abdullahi Tijjani Gwarzo.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto dai Jaridan National lens ba ta sami cikakkun bayanai kan shekarunsa, abin da ya haddasa rasuwarsa, da kuma lokacin da za a gudanar da jana’izarsa ba.
No comments