Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Tsohon Dalibin Jami'ar MAAUN Ya Kirkiri Manhajar Sada Zumunta

Tsofaffin daliban Jami’ar Maryam Abacha American University dake Maradi a jamhuriyyar kasar Nijer sun bayyana cewa sun kirkiri w...


Tsofaffin daliban Jami’ar Maryam Abacha American University dake Maradi a jamhuriyyar kasar Nijer sun bayyana cewa sun kirkiri wata manhaja wacce al'umma za su yi amfani da ita wajen sada zumunta a tsakaninsu. 

Manhajar wacce suka sanya wa suna da ‘Afrister’, sun ce manhaja ce da aka kirkira da za ta kawo sauyi wajen bai wa al'ummar damar kulla alaka da huldar zamantakewa. Sun kara da cewa an tsara manhajar ta yadda za ta haɓaka hulda a tsakanin daidaikun mutane, iyalai, abokai, da abokan kasuwanci, wanda zai haɓaka ʙwarewar masu amfani da manhajar.

An kirkiri manhajar ne a cikin shekarar 2021, a lokacin da Aliyu Ishaq da abokin aikinsa Alhassan Abubakar suke karatunsu a jami'ar MAAUN. 

A cewarsu Afrister ya sami karbuwa cikin sauri a wurin masu amfani da shi ganin yadda manhajar ta zo da sabbin abubuwa masu kayatarwa. 

A wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Abuja, Aliyu Ishaq ya danganta nasarar Afrister da irin horon da suka samu a  jami’ar Maryam Abacha.

Ya nuna matukar godiyarsa ga jami'arsa da ya kammala,  inda ya bayyana irin tasiri da jami'ar ta yi masa tare da sauran dalibai. 

Ya kuma yabawa wanda ya assasa jami'ar ta MAAUN, Farfesa Adamu Gwarzo bisa irin goyon baya da jagorancin da yake bayarwa.

Domin ganin sun samu yabo da karbuwa a duniya, Ishaq da abokin aikinsa sun ce suna aiki tuʙuru domin haɓaka Afrister, tare da tabbatar da cewa ya dace da ʙa'idodin da takwarorinsa na Yamma suka gindaya.

Ya kara da cewa, suna da himma da kuma kudurin yada Afrister a duniya, wanda ya ce idan suka yi hakan, za su samu wani gagarumin ci gaba a bangaren masana'antar fasaha da manhajar kulla zamantakewa.

No comments