Daga Abubakar Rabilu, Gombe Gamayyar Kungiyar Matasa ta ci gaban arewa maso gabas a jihar Gombe mai suna North East Coalitio...
Daga Abubakar Rabilu, Gombe
Gamayyar Kungiyar Matasa ta ci gaban arewa maso gabas a jihar Gombe mai suna North East Coalition of Youth for Progressive Governance and Sustainable Development’ ta kirayi tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin arziki Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami da ya amsa kiran su a shekarar 2027 wajen fitowa takarar gwamana a jihar
Kungiyar tayi wannan kiran ne ta bakin Sakataren ta na jihar Gombe Gideon Musa, a lokacin wani taron manema labarai da ta kira a ranar Asabar.
Yace su amincewa tsohon Ministan ne sakamakon irin dinbin Nasarorin da ya samar a lokacin da ya zama Darakta a hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa (NITDA) da kuma lokacin da ya ke ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani.
A cewar kungiyar, Pantami ya bai wa al’ummar jihar Gombe damar yin amfani da fasahar zamani ta hanyar bude cibiyoyin fasahar sadarwa ta zamani (ICT) a makarantu da sassa daban-daban na jihar inda aka horar da mutane tare da ba su damar shiga yanar gizo kyauta.
“Farfesa Pantami ne ya jagoranci samar da ofisoshi a fadin kasar nan ciki har da jihar Gombe a arewa maso gabas,tsohon ministan ya samar da ci gaba da samun dama ga ayyukan fasaha a yankin”
Sun kuma kara da cewa wadannan ofisoshin ba kawai inganta haɗin guiwa ba ne amma sun ba wa ma'aikatan jihar ƙarin dama don haɗin guiwa da dandalin kirkiro da musayar bayanai.", in ji shi.
Daga nan sai kungiyar ta yi kira ga tsohon ministan da ya amince da kiran da suka yi masa na ya fito ya tsaya takarar gwamnan jihar ta Gombe a zabe mai zuwa na shekarar 2027 sannan suka nemi gwamna Muhammad Inuwa Yahaya da ya mara masa baya a matsayin wanda zai gaje shi.
No comments