Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana aniyarsa ta dawo da masana'antar yadi da kuma bunƙasa noman auduga a jihar, b...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana aniyarsa ta dawo da masana'antar yadi da kuma bunƙasa noman auduga a jihar, bayan ziyarar da ya kai Yankin Masana'antu na Glo-Djigbe (GDIZ) da ke Jamhuriyar Benin tare da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da wasu gwamnoni.
Da yake jawabi bayan zagayen duba cibiyar masana'antun, Dauda Lawal ya ce abin da ya gani ya tuna masa da lokacin da masana'antar yadi ta Zamfara ke ɗaya daga cikin manyan hanyoyin samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arzikin jihar.
Ya bayyana cewa, ya taso ne a cikin yanayin wannan masana'anta, yana mai cewa mahaifinsa na daga cikin masu mallakar Masana'antar Yadi ta Zamfara, wadda a lokacin take gudanar da aiki sau uku a rana, inda kowane rukuni ke ɗaukar ma'aikata kusan 2,000.
Gwamnan ya ƙara da cewa, a wancan lokaci Zamfara na da masana'antun tace auduga guda 23 da kuma masana'antar sarrafa man auduga, inda har tsabar auduga ake sarrafawa zuwa man girki.
A cewarsa, nasarar da ya gani a yankin masana'antun na Glo-Djigbe ta ƙara masa ƙwarin gwiwa wajen dawo da sarkar darajar auduga gaba ɗaya, daga noma zuwa sarrafawa da kuma samar da kayayyakin yadi a Zamfara.
"Wannan ziyara ta nuna min hanya a fili. Dawo da wannan masana'anta na ɗaya daga cikin abubuwan da nake son bari a matsayin gadon mulkina a Zamfara, kuma na ƙuduri aniyar tabbatar da hakan," inji Lawal.
Ya bayyana cewa farfaɗo da masana'antar auduga da yadi ba wai kawai zai ƙarfafa manoma ba ne, har ma zai buɗe damammakin kasuwanci ga masu sarrafa kayayyaki da masana'antun cikin gida, tare da samar da dubban guraben aikin yi da inganta rayuwar al'ummar jihar.
Ziyarar ta kasance wani ɓangare na shirin Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kafa cibiyoyin sarrafa kayayyakin noma a sassa daban-daban na Nijeriya domin bunƙasa masana'antu da ƙara darajar albarkatun ƙasa.
No comments