Rahotanni daga Hedikwatar Tsaro (DHQ) ta Abuja sun bayyana cewa labarin da Brigediya Janar Ismaila Abdullahi (mai ritaya) ya rub...
Rahotanni daga Hedikwatar Tsaro (DHQ) ta Abuja sun bayyana cewa labarin da Brigediya Janar Ismaila Abdullahi (mai ritaya) ya rubuta, wanda ke cewa manyan jami'an sojoji sun bayar da gudunmawar kuɗi don kuɓutar da Brigediya Janar Mahrazu Tsiga (mai ritaya), wanda 'yan bindiga ke riƙe da shi, har na tsawon kwanaki 56, ba daidai ba ne.
A cikin sanarwa da Hedikwatar ta saki ta hannun Babban Daraktanta na Yaɗa Labarai, Brigediya Janar Tukur Gusau, sanarwar ta bayyana cewa aikin ceto an gudanar da shi ne kawai ta hannun sojojin da ke cikin rundunar musamman mai taken "Operation Fansar Yamma," waɗanda suka gudanar da cikakken bincike da aikin na ceto.
Maj-Gen Gusau ya bayyana cewa, "Hedikwatar Tsaro (DHQ) ta lura da labarin da Brigediya Janar Ismaila Abdullahi (mai ritaya) ya rubuta, wanda ke cewa manyan jami'an sojoji sun bayar da kudi don samun sakin Brigediya Janar Mahrazu Tsiga (mai ritaya), wanda aka riƙe na tsawon kwanaki 56.
"Wannan labari ya saɓawa da ƙoƙarin da sojojin Aikin Fansar Yamma suka yi domin gudanar da Aikin Bincike da Ceto don samun sakin Brigediya Janar Mahrazu Tsiga (mai ritaya)." A cewarsa.
Janar Gusau ya ƙara da cewa, "Ya kamata a fahimci cewa sace tsohon DG na NYSC ya faru ne a cikin daren 6 ga Fabrairu 2025, a Tsiga, yankin Kafur na Karamar Hukumar Bakori a Jihar Katsina.
Amma a daidai lokacin da aka sanar da sojojin rundunar 17, sun yi martani da wuri a kimanin ƙarfe 0300 (3 na safiya) na ranar da ita, kuma a cikin ƙwarewar aiki, sun tafi cikin sauri wajen bin sahu tare da Sashin Jiragen Sama na Aikin Fansar Yamma.
Waɗannan ƙoƙari sun hada da binciken luguden haramtattu da ke cikin Jeka, Areda, da Zango, duk a cikin Karamar Hukumar Kankara, a neman tsohon DG. Aikin ya wuce zuwa Ruwan Lafiya, Mununu, Matallawa da Bakkai a cikin Karamar Hukumar Faskari. Ko da yake ba a samu hulda da masu satar ba, sojojin sun yi nasarar matsa lamba kan ‘yan fashi, wadanda suka bar dabbobi da wasu wadanda aka sace a cikin gudun su." In ji shi.
No comments