Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Da Sannu Allah Zai Fallasa Masu Haddasa Rashin Tsaro A Zamfara -Gwamna Lawal A Sansanin Alhazai A Makkah

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya kai wa Alhazan jihar ziyarar ba-zata ta Barka da Sallah a ƙasar Saudiyya, inda ya buƙaci s...

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya kai wa Alhazan jihar ziyarar ba-zata ta Barka da Sallah a ƙasar Saudiyya, inda ya buƙaci su riƙa yi wa jihar addu'ar zaman lafiya da ɗorewar tattalin arziki, tare da neman Allah fallasa masu haddasa rashin tsaro a jihar.

A wani faifen bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta, an ga Alhazan na ta kabbara bayan shigowar gwamnan masaukin nasu.

A jawabinsa ga Alhazan, Gwamna Lawal ya ce, babu abin da zai ce musu sai godiya, wanda hakan ta sa ya ba su guzurin Barka da Sallah.

Gwamna Lawal ya ƙara da cewa, "Na gode wa Allah da ya sa dukkan Alhazan mu su na cikin ƙoshin lafiya kuma sun samun kulawa yadda ya kamata. Na ji daɗin ganin ku haka cikin farin ciki."

Ya ce, "Ina ƙara gode muku da irin addu'o'in da ku ke yi wa jihar mu da mu kan mu shugabanni. Allah Ya saka da alheri."

"Zan ƙara roƙon ku da ku ci gaba da yi wa ƙasa da Jihar Zamfara addu'a, mu ma shugabanni ku riƙa yi mana addu'a don mu riƙa yi muku gaskiya. Wannnan wuri ne da za a roƙi Allah Ya yaye mana dukkan matsalolin da mu ke fuskanta, musamman ma matsalar tsaro a Jihar Zamfara. Wannan dama ce da Allah ya ba mu, domin duk addu'ar da muka yi a wannan wuri mai tsarki karbabba ce," Gwamna Lawal ga alhazan."

Ya ci gaba da cewa, "Muna roƙon Allah Ya ƙasƙantar da duk wanda yake da hannu a matsalar tsaron Zamfara, ko wane ne shi. Allah Ya hana shi duk abin da yake nema, idan mulki ne ya hana shi, ya nisanta shi da duk wani abin alheri a rayuwar sa. Mun san akwai masu yi, amma Allah Ya fi su. Allah Ya fitar da al'ummar Zamfara daga matsalar nan ta tsaro.

"Na ya farin ciki yadda na gan ku, kuma ina tare da ku. Allah Ya karbi ibadun da muka yi da kuma wanda za mu yi a nan gaba, Ya yafe mana kura-kuran mu," in ji Gwamna Lawal.

Ya ce, "akwai wani ɗan guzuri da na umarci Shugaban Hukumar Alhazan Jihar da Mai Martaba su ba mahajjata na Riyal 375 (kimanin Naira 155,980.70) kowane mutum ɗaya a matsayin goron Allah daga waje na."

A nasa jawabin, Shugaban Hukumar Alhazan Jihar Zamfara, Alhaji Musa Mallaha, ya ce babu abin ya kamata al'ummar jihar su yi wa Gwamna Lawal sai addu'a, domin hakan zai ƙara ƙarfafa masa gwiwa wajen yaƙi da 'yan bindiga da gwamnatin sa ke yi.

Ya ce, "A madadin Alhazan jihar Zamfara su duba ɗaya da ɗari biyar da 'yan kai, mu na godiya bisa wannan girmamawa da ka yi mana ta tattaki domin ka kawo mana wannan ziyarar Barka da Sallah."

A nasu vangaren, mahajjatan jihar Zamfara sun bayyana jin daɗin su kan yadda Gwamna Lawal ya kula da su a duk inda suke a ƙasar Saudiyya.

Ɗaya daga cikin Alhazan, mai suna Alhaji Yusuf Abubakar Matsayi, ya ce, "Alhamdu lillahi, wannan gwamna ya kafa tarihi, don ya yi mana abubuwa na alheri, domin an kula da mu tun daga masaukin mu na Madina har Allah Ya kawo mu nan garin Makka.

"An ba mu masauki mai kyau tare da ingantaccen abinci. Mu shaida ne na irin faɗi-tashin da Gwamna Lawal ke yi na ganin an samu tsaro a Zamfara. Mu na fatan Allah Ya dafa masa, Ya sa ya mulki jihar Zamfara shekara huɗu sau biyu, ya gama lafiya."

Wata mahajjaciyar, Hajiya Umma Hassan ita ma ta bayyana farin cikinta da irin kulawar da Gwamna Lawal ya bai wa Alhazan.

Ta ce, "An haɗa mu da ƙwararrun ma'aikata da Malamai na ƙwarai domin su riƙa yi mana jagoranci. Duka Nijeriya babu gwamnan da ya fi na Zamfara ƙoƙari. Allah Ya taya shi riƙo."

No comments