Jihar Zamfara ita ce ta farko a Nijeriya da ta fara amfani da Tsarin Ilimin Fasahar Zamani (ZDLF) don samar wa al'ummarta mu...
Jihar Zamfara ita ce ta farko a Nijeriya da ta fara amfani da Tsarin Ilimin Fasahar Zamani (ZDLF) don samar wa al'ummarta muhimman fasahohin zamani don ci gaban tattalin arziki, tsarin gudanar da aiki na zamani, da ƙirƙire-ƙirƙire.
A ranar Larabar da ta gabata ne aka gudanar da babban taron masu ruwa da tsaki kan tsarin ilimin fasahar zamani na Zamfara a ɗakin taro na Garba Nadama a Sakatariyar JB Yakubu da ke Gusau, babban birnin jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa, taron masu ruwa da tsakin ya haɗa da manyan cibiyoyin gwamnatin tarayya, abokan ci gaba, ’yan majalisa, malamai, da shugabannin kamfanoni masu zaman kansu domin yin nazari tare da inganta tsarin.
A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya bayyana tsarin a matsayin wani kwakkwaran taswirar zamani da za a sa a gaba tare da jaddada aniyar gwamnatinsa na ganin an aiwatar da shi sosai.
Ya ci gaba da cewa, “A yau mun samu wani gagarumin ci gaba a tafiyarmu ta haɗin gwiwa a jihar Zamfara ta hanyar inganta fasahar zamani, ƙirƙire-ƙirƙire, da hanyoyin samun bayanai da fasahar sadarwa.
“Tsarin Ilimin Fasahar Zamani nna Zamfara wani tsari ne da zai amfani buƙatun al'umma na dogon lokaci don samar wa mutanenmu ƙarfin aiki da haɓaka ƙwarewarsu a cikin duniyar fasahar zamani.
"Kamar yadda muka sani, ilimin fasahar zamani yana da muhimmanci don samar da ayyukan yi da samar da ingantacciyar tsarin aiki. Ba zai yiwu mu rungume hannu mu bar jihar a baya ba a zamani ilimin fasahar zamani.
“Wannan tsarin yana da nufin samar da ilimi a bangaren fasahar zamani kan abubuwan da suma shafi - kwamfuta, ayyukan gwamnati, da kasuwanci. Tsarin yana dubi ga jihar da kowane ɗalibi zai ƙware sosai a fannin fasahar zamani, kowane ma'aikacin gwamnati zai samu fasahar zamani don gudanar da aikin sa, kuma manyan 'yan kasuwa da ƙanana suna da ƙwarewar faɗaɗa kasuwancinsu. Mun fara shirin aiwatar da wannan hangen nesa.
“Jihar Zamfara ta haɗa gwiwa da Kamfanin Oracle domin horar da matasa 3,000 a shirin 'Cloud 2 Computing, Artificial Intelligence, Data Science, and Database Management'. Tare da makarantar Oracle, manyan makarantunmu za su samu tallafi don yaye ɗalibai masu ƙwarewa a harkar masana’antu.
“An fara aiki a Cibiyar Fasahar Sadarwa ta Zamfara (ZIIT) da ke Gusau, wannan cibiya za ta kasance cibiyar ƙwararru ta yanki, da ke ba da ilimin kwamfuta da kuma samar da ƙirƙire-ƙirƙire a cikin gida. Muna da burin ganin mun ɗinke barakar fasahar zamani da kuma sanya Zamfara a matsayin cibiyar ilimin kwamfuta a Arewacin Nijeriya.”
Tun da farko, a jawabinsa na maraba sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Malam Abubakar Nakwada, ya bayyana ƙudirin gwamnatin jihar na ganin jihar Zamfara ta kasance kan gaba wajen kawo sauyi a bangaren fasahar zamani a Arewacin Nijeriya.
Da take isar da saƙon fatan alheri, Sanata Ikra Aliyu Bilbis (Sanata mai wakiltar Zamfara ta tsakiya), Shugabar Kwamitin Fasahar Zamani da Tattalin Arziki na Majalisar Dattawa, ta yaba wa Zamfara kan yadda take kan gaba a lokacin da ci gaban ƙasa ya ta'allaka kan fasahar zamani. Sanatar ta ba da gudunmawar kwamfutoci 300 ga ZITDA don tallafa wa tsarin fasahar zamani a duk faɗin jihar.
A jawabinsa dangane da Tsarin Ilimin Fasahar Zamani na Zamfara (ZDLF), Dokta Habib Gajam, Babban Sakatare na Hukumar Bunƙasa Fasahar Watsa Labarai ta Zamfara (ZITDA), ya bayyana tsarin a matsayin wata dabarar da ta shafi mutane da aka tsara.
Muhimman cibiyoyi na fasahar zamani na Gwamnatin Tarayya da aka wakilta a taron masu ruwa da tsakin sun haɗa da Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC), Galaxy Backbone, Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA), Cibiyar Kuka da Tauraron Ɗan Adam, da Hukumar Kare Bayanai ta Nijeriya (NDPC).
No comments