A yayin da Dr. Abba Ya'u yake cika shekara ɗaya da 'yan watanni a cikin office na shugaban ƙaramar hukumar Roni a jihar ...
A yayin da Dr. Abba Ya'u yake cika shekara ɗaya da 'yan watanni a cikin office na shugaban ƙaramar hukumar Roni a jihar Jigawa, mun waiwayi waɗansu ɓangarori na ayyukan da ya yi.
ƁANGAREN ILIMI
Tun kafin Dr. Abba Ya'u ya hau kan karagar Chairman na Roni, ya kasance wanda ya kafa Gidauniyar tallafawa marassa ƙarfi, ta hanyar biyan kuɗaɗen registration ga wasu daga cikin ɗalibai 'yan asalin ƙaramar hukumar.
Da Dr. Abba ya zama shugaban ƙaramar hukuma, sai hakan ya ƙara masa azama da jajircewa.
Bincikenmu ya tabbatar da cewa, Dr. Abba ya yi wa mutum 1238 registration, a yayin da 711 daga cikinsu kuma ya ɗauki nauyin karatunsu gaba ɗaya har su kammala. Waɗannan ɗaliban sun haɗa da waɗanda suke a Jami'a, Kwalejojin Ilimi da kuma makarantun lafiya na ciki da wajen jihar Jigawa.
ƁANGAREN RUWAN SHA
A ranar 16/12/2024 Dr.
ya tunkari matsalar ruwan sha gadan-gadan yi mata kwaf-ɗaya domin magance ta.
Ya fara da gyaran babbar cibiyar da ke bai wa garin ruwa da ta daina aiki, ya sabunta ta tare da zuba sabbin kayayyaki a cikinta. A yayin da ya ya gyara sololi guda talatin da biyar (35) a mazaɓu goma sha ɗaya (11) da ke Roni.
Dr. Abba Ya'u ya bayar da gudunmawa a ɓangarori mabambanta domin ci gabantar da ƙaramar hukumar Roni gaba da suka haɗa da lafiya, tsaro, noma da tallafawa masu ƙaramin ƙarfi da ayyukan alkairi.
Yusuf kabir Ɗan Jarida/Marubuci ne. Mai sharhi ne a kan al'amuran yau kullum, musamman siyasar Gabas ta Tsakiya. Yana rubutu a jaridun a ciki da wajen ƙasar Nijeriya.
kabiruyusuf533@gmail.com
No comments