Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Manyan Ayyuka A Tsafe Domin Farfaɗo Da Ci Gaban Al’umma

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sake jaddada cewa duk wani ci gaba da gwamnati za ta aiwatar dole ne ya kasance mai anfan...

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sake jaddada cewa duk wani ci gaba da gwamnati za ta aiwatar dole ne ya kasance mai anfani kai tsaye ga rayuwar al’umma, tare da samar da sauyi mai ma’ana.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da ya ƙaddamar da muhimman ayyuka biyar a Ƙaramar Hukumar Tsafe, a wani bangare na shirinsa na farfaɗo da inganta muhimman cibiyoyin jama’a a faɗin jihar.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, an bayyana cewa ayyukan da aka ƙaddamar sun haɗa da sabunta tashar mota ta zamani, gyaran kasuwa, gyaran makaranta, sabuntawa da kuma samar da kayayyakin aiki a babban asibitin Tsafe, da kuma gyaran fadar sarkin Tsafe.
A cewar sanarwar, waɗannan ayyuka suna taka muhimmiyar rawa a rayuwar al’umma, musamman a bangarorin shugabanci, kiwon lafiya, ilimi, kasuwanci da zirga-zirga, tare da ƙara danƙon zumunci da jin cewa jama’a na da hannu a ci gaban yankinsu.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Lawal ya ce sabunta fadar sarkin Tsafe alama ce ta girmama al’ada da kuma tabbatar da darajar masarautu a tsarin shugabanci na ƙasa. Ya ce sarakuna na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya, warware rikice-rikice da kuma haɗa kan al’umma.
Gwamnan ya ƙara da cewa, gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da masarautu a matsayin abokan hulɗa wajen sake gina Zamfara da dawo da martabar ta.

A bangaren ilimi da bunƙasa jarin ɗan Adam, ya bayyana cewa inganta Kwalejin Kiwon Lafiya ta Tsafe na nufin zuba jari ne a kan makomar ma’aikatan lafiya da za su yi hidima ga al’umma. A cewarsa, gyaran muhalli da kayan aikin makarantar zai ƙara inganta kwarewa da kwarin gwiwar ɗalibai.
Dangane da harkar lafiya kuwa, Gwamna Lawal ya ce sabunta babban asibitin Tsafe da samar masa da kayan aiki na zamani zai inganta ayyukan jinya, sauƙaƙa wa marasa lafiya da kuma taimaka wa ma’aikatan lafiya wajen gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Ya kuma jaddada cewa kasuwa da tashar mota na daga cikin ginshiƙan tattalin arzikin yankin, domin su ne ke haɗa manoma, ‘yan kasuwa, masu sana’o’i da sauran jama’a. Sabunta waɗannan wurare, in ji shi, zai inganta tsari, tsaro da kuma bunƙasa rayuwar jama’a.
Gwamnan ya yi kira ga sarakuna, shugabannin al’umma, ‘yan kasuwa, ma’aikatan lafiya da masu ruwa da tsaki da su ɗauki alhakin kula da waɗannan ayyuka domin su ɗore su ci gaba da anfani ga jama’a na dogon lokaci.

Ya ce duk inda jama’a suka ji cewa su na da hannu a dukiyar jama’a, to za su fi bada kariya da kulawa, wanda hakan zai tabbatar da ɗorewar ci gaba a faɗin jihar.

No comments