Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Jaridar THE SUN Ta Karrama Gwamnan Zamfara Da Lambar Yabo Ta ‘Gwamnan Shekarar 2025’

Gwaman Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya samu wata babbar karramawa bayan da jaridar The Sun ta ba shi lambar yabo ta “Gwamnan Shek...

Gwaman Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya samu wata babbar karramawa bayan da jaridar The Sun ta ba shi lambar yabo ta “Gwamnan Shekarar 2025”, sakamakon abin da aka bayyana a matsayin gagarumar nasara da gwamnatinsa ta samu a fannin shugabanci nagari.

An miƙa lambar yabon ne a wani gagarumin biki na Sun Awards da aka gudanar ranar Asabar, 31 ga Janairu, 2026, a ɗakin taro na Expo da ke Eko Hotels and Suites a Legas.
Bikin na shekarar-shekara na jaridar The Sun na karrama fitattun mutane ne da suka taka rawar gani a fannoni daban-daban na rayuwa a Nijeriya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa wannan karramawa wata shaida ce da ke nuna cewa manufofin Ayyukan Ceto Zamfara, wato “Rescue Mission” na gwamnatin Dauda Lawal suna kan turbar da ta dace.
Ya ce, tun bayan rantsar da gwamnan a ranar 29 ga Mayu, 2023, gwamnatin ta mayar da hankali wajen farfaɗo da Zamfara duk da ƙalubalen tattalin arziki da ta gada.

Sanarwar ta jaddada cewa bangaren tsaro ya kasance kan gaba a ajandar gwamnatin, inda aka kashe maƙudan kuɗaɗe domin inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Haka kuma, an nuna cewa an samu ci gaba mai ma’ana a fannoni kamar kiwon lafiya, ilimi, gina ababen more rayuwa, bunƙasa tattalin arziki da kula da jin daɗin ma’aikata.
Bugu da ƙari, gwamnatin Zamfara ta kuma yi fice a fannin kiwon lafiya a matakin farko, inda a watan Disambar bara aka ayyana jihar a matsayin wacce ta fi kowacce jiha a Arewa maso Yamma ƙwarewa a Gasar Jagorancin Kiwon Lafiya ta Matakin Farko.

Masu lura da al’amuran siyasa na ganin wannan lambar yabo a matsayin ƙarin kwarin gwiwa ga gwamnatin Zamfara, tare da ƙara jaddada muhimmancin ɗorewa kan manufofin da ke inganta rayuwar al’umma. A nasu bangaren, magoya bayan gwamnan na kallon karramawar a matsayin tabbacin cewa ƙoƙarin da Gwamna Lawal ke yi na samar da shugabanci nagari yana samun karbuwa har a matakin ƙasa.

No comments