Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana cewa jihar sa ba ta taba samun wani kuɗin tallafi daga Gwamnatin Tarayya ba tun bayan ha...
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana cewa jihar sa ba ta taba samun wani kuɗin tallafi daga Gwamnatin Tarayya ba tun bayan hawan sa mulki a shekarar 2023.
Ya bayyana haka ne a lokacin da gwamnoni ke tururuwar komawa APC mai mulki domin samun tagomashin Gwamnatin Tarayya.
Da yake zantawa da kafar yaɗa labarai ta DW Hausa, gwamnan PDP ɗin, ya ce akwai jihohi da suka samu maƙudan kuɗi daga Gwamnatin Tarayya.
Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa Zamfara ba ta samu ko sisi ba face kuɗin da doka ta tanada.
A cewar sa, “Gwamnatin Tarayya ba ta taba ba mu wani kuɗin tallafi ba kamar yadda ta yi wa wasu jihohi. Ina da sahihin bayani cewa wasu jihohi sun samu sama da Naira biliyan 500, amma jihata ba ta samu ko kobo ɗaya ba.”
Ya ƙara da cewa, yana ganin hakan na da alaƙa da kasancewar sa a jam’iyyar adawa, inda ya bayyana cewa, “Ina ganin hakan ne saboda ba mu jam’iyya ɗaya da su ba. Ni ina jam’iyyar adawa."
Rahotanni sun nuna cewa Gwamna Dauda Lawal ne kaɗai gwamna daga jam’iyyar adawa a yankin Arewa maso Yamma, yayin da sauran jihohin yankin ke ƙarƙashin APC.
Duk da haka, ya jaddada cewa rashin ƙarin tallafi daga tarayya bai hana gwamnatin sa aiwatar da ayyukan raya ƙasa ba.
Ya ce, "tun bayan da ya zama gwamna a 2023, ba su samu wani ƙarin tallafi daga gwamnatin tarayya ba baya ga abin da doka ta ware.
Gwamna Lawal ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ba ta karbi wani sabon bashi domin tafiyar da harkokin jihar ba, duk da ƙalubalen da ake fuskanta.
Ya ce, wannan na da alaƙa da bashin da gwamnatin da ta gabata ta karba, wanda har yanzu ake biya.
Game da makomarsa ta siyasa, gwamnan ya ce ba zai sauya sheƙa daga PDP nan take ba duk da matsalolin cikin gida da jam’iyyar ke fuskanta.
Kamar dai yadda muka sani, Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da a biya albashi da kuɗin fansho na watan Fabrairu cikin gaggawa kafin fara azumin watan Ramadan.
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan ya bayar da umarni ga Akanta Janar na jihar da ya saki kuɗin ba tare da bata lokaci ba domin ma’aikata da masu karbar fansho su samu sauƙin shirin azumi.
Wannan mataki na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da al’adu na jihar, Mahmud Dantawasa, ya sanya wa hannu a ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairun 2026.
No comments