Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Limamai 40 Sun Amfana Da Tagomashin Gwamna Dauda Lawal

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya raba motoci ga limamai 40 na masallatan Juma’a a faɗin jihar, a wani mataki da gwamnatin ...

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya raba motoci ga limamai 40 na masallatan Juma’a a faɗin jihar, a wani mataki da gwamnatin ta ce na daga cikin ƙoƙarinta na tallafa wa shugabannin addini domin sauƙaƙa musu gudanar da ayyukansu na wa’azi da hidima ga al’umma.

Da yake jawabi yayin rabon motocin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa manufar shirin ita ce inganta zirga-zirgar limaman da kuma ƙara musu damar kai saƙonnin addini da nasiha zuwa sassa daban-daban na al’umma.
Ya ce, Zamfara jiha ce da aka gina bisa tubalan addinin Musulunci, inda limamai ke taka muhimmiyar rawa wajen shiryar da jama’a a kan tafarkin gaskiya da adalci a dukkan ƙananan hukumomi 14 na jihar.

A cewarsa, kula da jin daɗin shugabannin addini na daga cikin abubuwan da gwamnatinsa ta bai wa muhimmanci. Ya bayyana cewa baya ga gina masallatai da gidaje ga limamai, gwamnati ta ga dacewar samar musu da hanyoyin sufuri domin sauƙaƙa musu zirga-zirga, musamman a ayyukan wa’azi da hulɗa da al’umma.
Gwamnan ya ce, an zabo limamai 40 a wannan mataki na farko, yana mai jaddada cewa shirin zai ci gaba a nan gaba domin faɗaɗa tallafin zuwa wasu limamai. Ya kuma roƙi malaman da su ci gaba da yi wa jihar Zamfara da Nijeriya baki daya addu’ar zaman lafiya mai ɗorewa da kwanciyar hankali.

Tun da farko, Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Addini, Sheikh Bello Almufty, ya yabawa Gwamna Lawal, yana mai cewa jagora ne mai gaskiya da kishin ci gaban kowa da kowa. Ya ce gwamnatin ta kawo sauyi mai ma’ana a rayuwar shugabannin addini ta hanyar inganta walwalarsu da alawus-alawus ɗinsu.
A madadin limaman da suka amfana, Sheikh Atiku Zawiyya ya nuna godiya ga gwamnan bisa wannan tallafi, yana mai cewa motocin za su taimaka wajen ƙara ƙarfin ayyukan wa’azi da hidima ga jama’a. Ya yi addu’ar Allah ya ƙara bai wa gwamnan ikon ci gaba da ayyukan alheri, yana mai cewa irin wannan kyauta na buƙatar lada daga Allah.
Limaman da suka amfana sun kuma sha alwashin ci gaba da yaɗa saƙon zaman lafiya, haɗin kai da kyawawan ɗabi’u a cikin al’ummominsu.

No comments