Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Ƙungiyar Matasan Baburawa Sun Gudanar Da Taron Bunƙasa Cigaban Al’ummarsu A Kano

Daga Ibrahim Muhammad, Kano Ƙungiyar al’ummar Baburawa mazauna Kano ta gudanar da taron shugabannin ƙungiyoyinta na sassa daban-...

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Ƙungiyar al’ummar Baburawa mazauna Kano ta gudanar da taron shugabannin ƙungiyoyinta na sassa daban-daban na jihar a ranar Asabar, a makarantar Special Primary School da ke unguwar Brigade.

Taron ya gudana ƙarƙashin jagorancin Sarkin Samarin Baburawa na jihar Kano, Alhaji Hassan Aliyu, inda ya samu halartar ‘yan ƙabilar daga wurare daban-daban na faɗin jihar.

Da yake zantawa da manema labarai a gefen taron, Sarkin Matasan Baburawan Kano, Alhaji Hassan Aliyu, ya ce an shirya taron ne domin bai wa matasa damar fahimtar inda aka dosa, tare da sauraron ra’ayoyinsu da shawarwarinsu kan yadda za a tunkari gaba, domin samar wa ƙungiyar Baburawa (ABURWA) shugabanci mai inganci da zai dace da zamani.

Ya yi nuni da cewa ƙungiyar al’ummar Baburawa ta shafe sama da shekaru 75 a Kano, amma ana samun wasu ‘yan ƙungiyar da ke aikata abubuwan da bai kamata ba, ba tare da an ɗauki mataki a kansu ba. Ya ce idan aka cigaba da hakan, zai iya janyo koma baya, amma idan ana ladabtarwa, hakan zai zama darasi ga sauran mambobi, kuma zai taimaka wajen samun ci gaba.

Sarkin Samarin Baburawa na jihar Kano ya ƙara da cewa, a matsayinsu na wakilan matasa, suna iya yin iyakacin ƙoƙarinsu wajen haɗa kan matasa da kuma wayar musu da kai kan tafiyar ƙungiyar, domin tabbatar da cewa ‘ya’yansu da jikokinsu za su amfana da ita a nan gaba. 

Ya jaddada buƙatar a samu sauyi mai kyau da zai kai ga cigaba ɗari bisa ɗari.

Ya ce taron ya yi tasiri matuƙa, inda yawan mahalarta ya zarce hasashen da suka yi. 

Ya gode wa Allah da kuma mahalarta taron bisa haɗin kai da suka bayar, yana mai cewa kowa ya bayar da tasa gudunmawar, wanda za a tattara a duba a kuma aiwatar da muhimman daga ciki.

Alhaji Hassan Aliyu ya bayyana cewa a halin yanzu suna da sama da ɓangarori guda 10 na ƙungiyar Baburawa a jihar Kano, kuma kowanne na gudanar da ayyukansa yadda ya kamata, lamarin da ke faranta masa rai a matsayinsa na Sarkin Matasan Baburawan Kano. 

Ya ce daga cikin shawarwarin da aka bayar akwai buƙatar ƙara himma wajen bunƙasa zamantakewar Baburawa a jihar Kano, domin hakan zai ƙara fito da su fili. 

Ya ƙara da cewa taron da aka gudanar na daga cikin ƙoƙarin da ake yi domin a san da su tare da tabbatar da tafiyar ƙungiyar ta tafi yadda ake buƙata.

Don haka ya yi kira ga al’ummar Baburawa mazauna Kano da su tashi tsaye su shiga cikin ƙungiyar (ABURWA), yana mai cewa idan mutum yana cikin ƙungiya ana saninsa, amma idan bai shiga ba, hakan na iya haifar da matsala.

Saboda haka ya buƙaci waɗanda ba su shiga ƙungiyar ba da su zo su hada kai da ‘yan uwansu.

A ƙarshe, ya bayyana cewa akwai kyakkyawar dangantaka ta zamantakewa da auratayya tsakanin Baburawa da Hausawa a Kano. 

Ya ce ana samun iyalai da suka haɗa jini, inda wani mahaifinsa Babur ne mahaifiyarsa Bahaushiya, ko akasin haka, lamarin da ya sa suka zama tamkar tsintsiya maɗaurinki ɗaya. 

Ya kuma jaddada cewa babu wani gari a Nijeriya da ya karɓi Baburawa da yawa kamar jihar Kano.

No comments