Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su ƙara himma wajen yin addu’o’i domin tabbatar da zaman l...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su ƙara himma wajen yin addu’o’i domin tabbatar da zaman lafiya a jihar Zamfara da kuma ƙasa baki ɗaya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake taya Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan na kwanaki 30, tare da shiga bukukuwan Sallah Ƙaramar (Eid-el-Fitr), wadda ke nuna ƙarshen watan ibada da tsarkakewar ruhi.
A cikin saƙonsa na barka, Gwamna Lawal ya jaddada muhimmancin wannan lokaci na Sallah, yana mai cewa lokaci ne na farin ciki, godiya ga Allah, haɗin kai da kuma sabunta niyya.
Ya ƙara da cewa wannan lokaci na bukukuwa ya kamata ya zama wata dama ta ƙara tashi tsaye wajen neman zaman lafiya da haɗin kan al’umma.
“Ina taya ɗaukacin al’ummar Musulmi a Zamfara da Nujeriya murnar kammala azumin watan Ramadan na kwanaki 30, tare da shiga bikin Eid-el-Fitr, wato ranar buɗe baki. Wannan lokaci ne na farin ciki da godiya, kuma ya kamata mu ƙara dagewa da addu’o’i domin zaman lafiya a jiharmu da ƙasarmu,” inji shi.
Gwamnan ya bayyana cewa azumin Ramadan da aka kammala yana da muhimmiyar rawa wajen koyar da haƙuri, ladabi, tausayi ga juna da kuma kusantar Allah, yana mai cewa waɗannan darussa su ne ginshiƙan gina al’umma mai nagarta.
Ya kuma jaddada cewa domin a samu ci gaba mai ɗorewa a Zamfara da Nijeriya, wajibi ne al’umma su haɗa kai, su rungumi juna tare da ɗaukar nauyin kula da juna, domin samar da makoma mai kyau ga kowa.
A ƙarshe, Gwamna Lawal ya yi addu’ar Allah Ya sa a gudanar da bukukuwan Sallah cikin lumana da kwanciyar hankali, tare da fatan samun ƙoshin lafiya, zaman lafiya da bunƙasar tattalin arziki a shekaru masu zuwa.
SALLAH ƘARAMA: Gwamna Lawal Ya Buƙaci Musulmi Su Ƙara Addu’o’in Zaman Lafiya

No comments