Gwamnatin Jihar Zamfara ta shirya tare da ɗaukar nauyin auren gata ga mutum 100 da aka zabo daga rukunin marasa ƙarfi a dukkan ƙ...
Gwamnatin Jihar Zamfara ta shirya tare da ɗaukar nauyin auren gata ga mutum 100 da aka zabo daga rukunin marasa ƙarfi a dukkan ƙananan hukumomi 14 na jihar.
Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa wannan shiri na daga cikin ƙudirin gwamnatinsa na tallafa wa marasa galihu da inganta rayuwarsu ta hanyar tsare-tsare masu amfani.
Ya bayyana hakan ne ta bakin Mataimakin Gwamna, Mani Mummune, wanda ya wakilce shi a wajen bikin.
A cewarsa, gwamnati za ta ci gaba da ɗaukar matakan da za su taimaka wajen ɗaukaka rayuwar jama’a, musamman waɗanda ke cikin buƙata.
Ya ƙara da cewa, gwamnati ta biya sadaki na Naira 200,000 ga kowace amarya, tare da ba su tallafin Naira 50,000 domin fara ƙananan sana’o’i a gidajen aurensu.
A wajen taron, Sarkin Kaura Namoda, Alhaji Sanusi Muhammad Asha, ya wakilci amaren inda ya aurar da su ga mazajensu bisa ga ƙa’idojin addinin Musulunci.
Gwamnan ya kuma miƙa takardun shaidar aure da kayayyakin more rayuwa ga ma’auratan, tare da yi musu nasiha kan muhimmancin girmama juna da zaman lafiya a gidajensu domin samun albarkar Allah.
“Ku girmama juna, ku zauna lafiya domin gina gidaje nagari da za su jawo albarkar Ubangiji,” in ji shi.
Rahotanni sun nuna cewa wasu manyan jami’an gwamnati sun haɗa kai wajen bayar da gudunmawar Naira miliyan 5 domin tallafa wa sabbin ma’auratan.
A wani bangare kuwa, Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Zamfara, Sheikh Umar Hassan, ya yaba da wannan shiri na gwamnati, tare da jinjinawa kokarin gina ofisoshin dindindin na hukumar a dukkan kananan hukumomi, wanda ya ce zai kara inganta ayyukan hukumar da kuma hidima ga al’umma.
No comments