Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Yadda Gwamnan Zamfara Ya Kwantar Da Hankalin 'Yan Gudun Hijira A Tsafe

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya ci karo da wasu 'yan gudun hijira masu zanga-zanga a yankin Ƙaramar Hukumar Tsafe, inda...

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya ci karo da wasu 'yan gudun hijira masu zanga-zanga a yankin Ƙaramar Hukumar Tsafe, inda ya tsaya da tawagar sa ya saurari koken jama'a, sannan ya yi jawabai masu tsara jiki.

'Yan gudun hijirar sun fito ne daga ƙauyukan da suka haɗa da Gajin Zama, Dakolo, Ƙurar Mota Gunja da sauran wasu Ƙauyukan da 'yan ta'adda suka addaba, sun datse babban titi da ke zuwa Funtua daga Gusau.
Mutanen sun yi kira ga hukumomi da masu ruwa da tsaki a harkar Tsaro su kai masu É—aukin gaggawa saboda tsananin bala'in da suke ciki na matsin lamba daga 'yan ta'adda.

A lokacin da ya iso wurin da 'yan gudun hijirar ke zang-zangar, Gwamna Lawal ya fito daga cikin motar sa ya saurare su, inda ya yi masu taƙaitaccen jawabin da ya sanyaya masu rai.

Cikin jawabin nasa, Gwamnan ya tabbatar masu da cewa gwamnatin sa na iyaka ƙoƙarin ta, kuma ba za ta gajiya ba, wajen ganin an samu zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.

 Daga nan ya yi alÆ™awarin kulawa da su a inda su ke, wajen ba su abinci da sauran kayan buÆ™atu, tare da ba su tabbacin tura jami'an tsaro a waÉ—annan yankuna na su don fatattakar waÉ—annan 'yan ta'adda.

No comments