Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Gwamnatin Tinubu Ta Ƙaddamar Da Cibiyar Horar Da Masana Motoci A Gusau, Matasa 100 Sun Amfana

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ƙaddamar da sabuwar Cibiyar Ƙira da Bunƙasa Masana’antar Motoci ta Ƙasa a Gusau, babban birnin Ji...

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ƙaddamar da sabuwar Cibiyar Ƙira da Bunƙasa Masana’antar Motoci ta Ƙasa a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, tare da horar da matasa 100 kan fasahar sarrafa na’urori ta zamani, domin ba su ƙwarewar gyaran babura da adaidaita sahu masu amfani da man fetur da kuma iskar gas ta CNG.

An ƙaddamar da cibiyar ne a ranar Alhamis ta hannun Karamin Ministan Masana’antu na Tarayya, Sanata John Owan Enoh, a wani shiri da ya samu haɗin gwiwar Cibiyar Ƙira da Bunƙasa Masana’antar Motoci ta Ƙasa (NADDC) da Ofishin Shirin Musamman na Made in Nigeria a Jihar Zamfara.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa an kafa irin waɗannan Cibiyoyin Horar da Masana Motoci a dukkan shiyyoyin Nujeriya guda shida domin tabbatar da cewa matasa a faɗin ƙasar sun samu damar koyon sana’o’in zamani da kuma samun ayyukan yi.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa ci gaban da ake samu a fannin fasahar sarrafa na’urori ta zamani, motocin lantarki, fasahar makamashi madadin fetur, na’urorin gano matsaloli na zamani da tsarin dijital suna sauya fasalin harkokin sufuri a duniya.
Gwamnan ya yabawa Cibiyar Ƙira da Bunƙasa Masana’antar Motoci ta Ƙasa (NADDC) bisa irin gudunmawar da take bayarwa wajen bunƙasa ƙwarewar matasa da kuma ƙarfafa masana’antar ƙera motoci a Nijeriya.

Ya ce: “A matsayina na gwamna, na yi imani cewa makomar kowace al’umma tana hannun ilimi, ƙirƙire-ƙirƙire da kuma bunƙasa jarin ɗan Adam. Saboda haka wajibi ne matasanmu su samu ƙwarewar da za ta ba su damar yin gogayya a kasuwar aiki ta duniya.”

Gwamna Lawal ya tunatar da mahalarta taron cewa bayan hawansa mulki a shekarar 2023, ya kai ziyara hedikwatar NADDC da ke Abuja domin neman haɗin gwiwa wajen horas da matasan Zamfara sana’o’in gyaran motoci da fasahohin zamani.

Ya bayyana cewa yaƙi da talauci, rashin aikin yi da matsalar tsaro ba zai yiwu ba sai an bai wa matasa ilimi da sana’o’in da za su dogara da kansu.
A nasa jawabin, Ƙaramin Ministan Masana’antu na Tarayya, Sanata John Owan Enoh, ya ce Gwamnatin Tarayya ta ƙara ƙaimi wajen tattaunawa da masu zuba jari na ƙasashen waje da manyan kamfanonin kera motoci domin kafa cibiyoyin masana’antar motoci da faɗaɗa samar da kayayyakin cikin gida a Nijeriya.

Ya ce, wannan mataki zai taimaka wajen ƙarfafa tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma rage dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.

Gwamna Lawal ya kuma jaddada cewa kafa cibiyar a Zamfara ya yi daidai da manufar Ajandar Sabonta Fata ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wadda ke mayar da hankali kan bunƙasa matasa, inganta masana’antu da kuma amfani da makamashi mai tsafta ta hanyar shirin amfani da iskar gas ta CNG na Shugaban Ƙasa.

Ya ƙara da cewa, cibiyar za ta buɗe sabbin damammaki ga matasan jihar wajen samun sana’a, ƙirƙire-ƙirƙire, dogaro da kai da kuma inganta rayuwarsu.

No comments