Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa ci gaban al'umma ba zai tabbata ba sai idan ana tafiyar da albarkatun ƙa...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa ci gaban al'umma ba zai tabbata ba sai idan ana tafiyar da albarkatun ƙasa cikin gaskiya, adalci da inganci, tare da samar da yanayi mai kyau da zai bai wa masu zuba jari damar gudanar da harkokin su cikin bin doka.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin ƙaddamar da Matatar Haƙowa da Sarrafa Ma'adinin Lithium ta Zamfara da ke ƙauyen Boko, a Ƙaramar Hukumar Zurmi.
An gina matatar ne ta hannun haɗin gwiwar kamfanonin ZAM Mining Company Ltd, Bima Mines Ltd, Jinlide Mining Co. Ltd da wasu abokan hulɗa, kan kuɗin da ya kai dala miliyan 200.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Lawal ya ce ƙaddamar da matatar wata sabuwar kafa ce ta bunƙasa arzikin Zamfara ta hanyar jawo ingantattun masu zuba jari, haɓaka masana'antu, samar da ayyukan yi da kuma amfani da albarkatun ma'adinai ta hanya mai ɗorewa, tare da sanya jin daɗin al'umma a gaba.
Ya ce, tsawon shekaru, Zamfara ta yi fice a matsayin jihar da Allah Ya albarkace ta da ɗimbin albarkatun ma'adinai, amma ya jaddada cewa ainihin albarkar ba ta ta'allaƙa da kasancewar ma'adinan ba, sai dai yadda ake amfani da su wajen inganta rayuwar jama'a.
A cewarsa, tun bayan hawan gwamnatinsa mulki, ta ƙuduri aniyar sauya tsarin harkokin ma'adinai a jihar daga ayyukan da ba su da tsari zuwa ingantaccen tsari na doka, daga anfani ba tare da ƙara ƙima ba zuwa ƙirƙirar darajar tattalin arziki, da kuma daga asarar damammaki zuwa rabon arziki ga jama'a.
Gwamnan ya ce saboda haka ne gwamnatin jihar ke ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da za su ƙarfafa haƙar ma'adinai bisa doka, jawo sahihan masu zuba jari, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya domin tabbatar da cewa harkokin ma'adinai suna bayar da gudunmawa ga ci gaban tattalin arziki.
Lawal ya ƙara da cewa tattalin arzikin duniya na sauyawa cikin sauri, inda lithium da sauran muhimman ma'adinai suka zama ginshiƙi wajen samar da makamashi mai sabuntawa, motocin lantarki, fasahohin zamani da bunƙasa masana'antu.
Ya ce Zamfara ba za ta ci gaba da kasancewa mai fitar da ɗanyen ma'adinai kaɗai ba, illa sai ta shiga cikin dukkan sassan sarrafa su domin ƙara musu ƙima.
A cewarsa, kafa wannan matata ya yi daidai da manufar gwamnatinsa ta mayar da hankali kan sarrafa ma'adinai a cikin gida, ƙara musu ƙima, horas da matasa ƙwarewa da bunƙasa masana'antu.
Gwamnan ya kuma tabbatar wa sahihan masu zuba jari cewa gwamnatin Zamfara za ta ci gaba da samar musu da yanayin da zai ba su damar gudanar da harkokinsu cikin nasara.
Ya ce gwamnati za ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa wajen tsaro, inganta ababen more rayuwa da kuma tsara manufofin da za su tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.
Hakazalika, ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta amince da duk wani aikin haƙar ma'adinai da ya saɓa wa doka ko wanda zai lalata muhalli ba, yana mai cewa dole ne al'ummomin da ke zaune a yankunan da ake haƙar ma'adinai su amfana kai tsaye.
Lawal ya yi kira ga al'ummar ƙauyen Boko da maƙwabtansu da su ɗauki wannan jari a matsayin haɗin gwiwa domin ci gaba.
Ya kuma umarci kamfanonin da ke gudanar da aikin da su bai wa mazauna yankin fifiko wajen samar da ayyukan yi, horas da su sana'o'i, gudanar da ayyukan raya al'umma, kare muhalli da kuma cika nauyin da kamfanoni ke da shi na taimakawa al'umma.
A ƙarshe, Gwamna Lawal ya taya duk masu ruwa da tsaki da suka taka rawa wajen tabbatar da wannan aiki murna, kafin ya ayyana a hukumance buɗe Matatar Haƙowa da Sarrafa Ma'adinin Lithium ta Zamfara.
No comments