Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya samu babbar lambar yabo ta ZIK International Peace and Leadership Award a ƙasar Ghana, bi...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya samu babbar lambar yabo ta ZIK International Peace and Leadership Award a ƙasar Ghana, bisa la’akari da nasarorin da gwamnatinsa ta samu cikin shekaru uku da suka gabata.
A wata sanarwar da Sulaiman Bala Idris Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa, an gudanar da bikin bayar da lambar yabon karo na bakwai na ZIK International Peace and Leadership Award ne a ranar Juma’a a Cibiyar British Council da ke Accra, babban birnin Ghana.
Taken babban taron na bana shi ne: “Jagoranci, Zaman Lafiya da Haɗin Kan Yankuna: Bunƙasa Ci gaban Afirka a Tsarin Duniya Mai Sauyawa.”
Kwamitin amintattu da majalisar gudanarwar lambar yabon sun bayyana cewa, daga cikin dalilan da suka sa suka karrama Gwamna Dauda Lawal akwai gagarumin ci gaban da gwamnatinsa ta samu a fannin jagorancin ɓangaren gwamnati da sauye-sauyen tattalin arziki a Zamfara.
Shugaban Kwamitin Amintattu (BOT) na ZIK Pan-African Award, Farfesa Echefuna R.G. Onyeabadi, ya ce manufar lambar yabon ita ce karrama mutanen da ke bayar da gagarumar gudunmawa wajen yi wa al’umma hidima.
Da yake jawabi bayan karɓar kyautar, Gwamna Dauda Lawal ya nuna godiyarsa ga masu shirya taron, tare da alƙawarin ƙara ƙoƙari wajen ceto da sake gina Jihar Zamfara.
Gwamnan ya ce, “Ina sadaukar da wannan lambar yabo ga ɗaukacin al’ummar Jihar Zamfara. Gwamnatina ta shafe shekaru tana aiki tuƙuru domin tabbatar da cewa Zamfara za ta iya gogayya da kowace jiha a Nijeriya. Wannan shi ne alƙawarin da muka ɗauka, kuma cikin shekaru uku kacal mun zarce abin da mutane suke tsammani.”
Ya ce gwamnatinsa ta kawo sauye-sauye a Zamfara ta hanyar shirye-shiryen sabunta birane, tare da gina sabon filin jirgin sama na zamani, wanda ya ce ba a taɓa samun makamancinsa ba a jihar tsawon sama da shekaru 30 tun bayan kafuwarta.
Gwamna Lawal ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta samu ci gaba a fannoni da dama, ciki har da tsaro, gyaran ma’aikatun gwamnati, ilimi, kiwon lafiya da sauran muhimman ɓangarorin ci gaban al’umma.
Ya ce, “Ina matuƙar godiya ga masu shirya wannan babban taron karatu da bayar da kyaututtuka na shekara-shekara. Wannan karramawa na da muhimmanci sosai a gare ni, kuma za ta ƙara mani ƙwarin gwiwar yin abubuwa da dama domin al’ummata. Zamfara na kan hanyar ci gaba.”
Daga cikin sauran manyan baƙi da aka karrama a wajen taron har da Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi A. Sule, wanda aka ba shi lambar yabon ne bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen hidimar jama’a da samun ci gaba mai ɗorewa.
No comments