Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

CIKA SHEKARA 58: Shugaban Jam’iyyar APC Na Ƙasa, Mutum Ne Mai Son Ci Gaba -Gwamnan Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya taya Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, murnar zagayowar ranar hai...

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya taya Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Farfesa Nentawe Yilwatda, wanda ya taɓa riƙe muƙamin Ministan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, ya cika shekaru 58 a ranar Asabar, 8 ga Agusta, 2026.

Gwamna Lawal ya bayyana shugaban jam’iyyar a matsayin wani muhimmin jigo ga tafiyar masu kishin ci gaba da kuma siyasar Nijeriya.

A cikin saƙon taya murnar, Gwamna Lawal ya ce, “A wannan rana ta zagayowar ranar haihuwarsa, ina taya shugabanmu, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, murnar cika shekaru 58. ƙwararren malami ne kuma jagoran jam’iyya mai kishin ci gaba, wanda ya sanya bunƙasa Jam’iyyar APC a gaba.

“Jagoranci na gari da hangen nesan da Farfesa Nentawe ya nuna sun taka muhimmiyar rawa wajen inganta manyan tsare-tsare da kuma ƙarfafa haɗin kai da fahimtar juna tsakanin mambobin babbar jam’iyyarmu.

“Yayin da kake cika shekaru 58 a yau, ina maka fatan ƙarin shekaru masu yawa cikin cikakkiyar lafiyar hankali, jiki da zamantakewa, domin Nijeriya ta ci gaba da amfana da ɗimbin ilimi da ƙwarewar da kake da su.”

Gwamna Lawal ya kuma yaba da yadda Farfesa Nentawe ya gudanar da zaɓukan fidda gwani na APC na baya-bayan nan, yana mai cewa yadda ya tafiyar da su ya nuna iliminsa, ladabinsa, gaskiyarsa da kuma jajircewarsa wajen tabbatar da abin da ya dace.

Gwamnan ya yi fatan Allah Ya ƙara wa shugaban jam’iyyar lafiya da tsawon rai, tare da ci gaba da ba shi damar bayar da gudunmawa ga jam’iyyar da ci gaban Nijeriya, kamar yadda yake ƙunshe cikin wata sanarwa da Sulaiman Bala Idris
Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara ya sa wa hannu.

No comments