Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi Ya Yaba Da Ayyukan Gwamna Dauda Lawal

Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sunusi na II, ya bayyana gamsuwarsa da irin ayyukan raya ƙasa da Gwamna Dauda Lawal k...

Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sunusi na II, ya bayyana gamsuwarsa da irin ayyukan raya ƙasa da Gwamna Dauda Lawal ke gudanarwa a Jihar Zamfara.

Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin bikin Ć™addamar da sabon ginin Masallacin Zawiyya da makarantar Islamiyya da aka gyara tare da samar musu da kayan aiki a Gusau, babban birnin jihar, ranar Juma’a.

Sanarwar ta fito ne daga bakin Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, a ranar 8 ga Nuwamba, 2026.

Masallacin Zawiyya na daga cikin tsofaffin cibiyoyin addinin Musulunci a Zamfara, wanda ya shahara wajen samar da fitattun malamai a fannoni daban-daban na ilimin addini da sauran ɓangarorin karatu.

A yayin huÉ—ubar sallar Juma’a da aka gudanar a sabon masallacin, Farfesa Ibrahim Maqari ya jaddada muhimmancin zaman lafiya da kyautata zamantakewa tsakanin al’umma, tare da yin kira ga Musulmi da su ba da muhimmanci wajen tsafta, musamman a wuraren ibada.

Da yake jawabi a wajen bikin ƙaddamarwar, Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sunusi na II, ya ce mutanen da suka san irin tsohon ginin Zawiyya ne kawai za su iya fahimtar girman aikin da ingancin gyaran da Gwamna Lawal ya gudanar.

Ya kuma jaddada cewa wajibi ne al’umma su kula da sabon masallacin, ta hanyar tabbatar da tsaftarsa da kuma kiyaye shi daga lalacewa.

A kalamansa, Sarkin ya ce: “Ya kamata a riĆ™a kiyaye tsaftar wannan masallaci tare da tabbatar da cewa yana cikin yanayi mai kyau. Dole ne mu kula da tsafta a duk lokacin da muka zo nan, domin masallaci alama ce ta Musulunci.

“Na ji daÉ—in wannan aiki matuĆ™a. Ina roĆ™on Allah MaÉ—aukakin Sarki Ya saka wa Mai Girma Gwamna da alheri.

“Ina ganin kyawawan ayyukan da kuke gudanarwa a Jihar Zamfara a É“angarorin ilimi, kiwon lafiya, tsaro da samar da ababen more rayuwa.

“Ban yi mamaki ba, domin na san gwamnan tun lokacin da yake harkar banki. Na san irin Ć™warewarsa da basirarsa, kuma ina matuĆ™ar jin daÉ—in yadda yake gudanar da mulkinsa tare da ayyukan alheri da yake yi a matsayin gwamna.”

Sarkin ya ce yana farin ciki da ganin yadda Gwamna Dauda Lawal ke amfani da ƙwarewarsa wajen kawo ci gaba a jihar, yana mai nuna jin daɗinsa kan irin ayyukan da gwamnan ke gudanarwa.

No comments