Al’ummar garin Talata Mafara sun fito kwansu da kwarkwatarsu a ranar Litinin, yayin da reshen jam’iyyar APC na Jihar Zamfara ya ...
Al’ummar garin Talata Mafara sun fito kwansu da kwarkwatarsu a ranar Litinin, yayin da reshen jam’iyyar APC na Jihar Zamfara ya ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna na shekarar 2027.
An gudanar da babban taron ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen ne a babban filin sallar idi da ke Ƙaramar Hukumar Talata Mafara.
Sanarwar da mai magana da yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar 23 ga Nuwamba, 2026, ta ce taron ya samu gagarumar halartar magoya bayan jam’iyyar daga sassa daban-daban na jihar.
Taron ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar APC a jihar, ciki har da Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na Tinubu da Shettima, da tsohon Gwamnan Zamfara, Abdul’aziz Yari, da kuma tsofaffin gwamnonin jihar, Ahmad Sani Yarima da Mahmud Aliyu Shinkafi, tare da sauran manyan ’yan jam’iyyar.
A cewar sanarwar, Dubban mambobi da magoya bayan APC ne suka tarbi manyan baƙin, lamarin da ke nuna irin farin jinin da Gwamna Dauda Lawal ke da shi a jihar.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Lawal ya bayyana farin cikinsa bisa yawan mutanen da suka halarta, tare da gode wa al’ummar Talata Mafara bisa gagarumar tarbar da suka yi masa da sauran jiga-jigan jam’iyyar.
Gwamnan ya kuma yi tsokaci kan muhimman ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ta aiwatar a Ƙaramar Hukumar Talata Mafara, yana mai cewa an kammala ayyuka sama da 40 a yankin.
A cikin jawabinsa, Lawal ya ce ya halarci taron ne domin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna na jam’iyyar APC, tare da neman goyon bayan al’umma domin sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu da shi kansa a matsayin gwamnan jihar.
Ya kuma nemi jama’a da su zaɓi ’yan takarar APC a dukkan matakan zaɓe, daga sama har ƙasa, yana mai cewa yawan mutanen da suka halarci taron ya tabbatar masa da cewa Talata Mafara na tare da jam’iyyar.
Gwamnan ya ce, “Na aiwatar da ayyuka sama da 40 a Ƙaramar Hukumar Talata Mafara. Ayyukan sun haɗa da sake gina Babban Asibitin Talata Mafara tare da samar masa da kayan aikin likitanci, da kuma wasu ayyuka da dama a Jami’ar Jihar Zamfara.
“Muna da ingantaccen shirin raya ƙasa wanda kuka gani da kanku ta hanyar ayyukan da muka gudanar. Zan ci gaba da ƙara yin ayyukan alheri idan kuka sake zaɓena a matsayin gwamnan Jihar Zamfara.”
Ya sake jaddada cewa gwamnatinsa na da wani tsari na ci gaba da aiwatar da ayyukan raya ƙasa, idan har al’ummar jihar suka ba shi damar ci gaba da jagorantar su bayan zaɓen 2027.

No comments