Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Matakan Kare Kai Daga Sanyin Hunturu

Akasari idan lokacin sanyi ya kama, mutane kan yi ƙoƙarin magance lamarin ta hanyar ɗaukar wasu matakai musamman ta hanyar sauya...


Akasari idan lokacin sanyi ya kama, mutane kan yi ƙoƙarin magance lamarin ta hanyar ɗaukar wasu matakai musamman ta hanyar sauya sutura da kuma irin abincin da suke ci.

Farfesa Isa Sadiq Abubakar ƙwararren likita ne a asibitin koyarwa na Aminu Kano kuma ya shawarci mutane da su dinga yin amfani da kaya masu kauri da da za su kare su daga yanayin.

"Kada ya zamana cewa mutane su dinga zama da bangarorin jikinsu a bude, musamma wajen kawunansu, yana da kyau a sanya hula ko dan kwali, ko kuma wani lokaci idan sanyi ya yi yawa har wuya ma ya kamata a rufe ta hanyar amfani da abu mai kama da rawani," in ji shi.

"Wannan yana taimakawa wurin ɗumama jiki."

Ya ƙara da cewa saboda ƙura, mutane na iya amfani da takunkumin fuska, ko kuma abin da ake rufe baki domin kada ƙura ta riƙa yawan shiga ta hanci, "abin da ka iya rage matsaloli musamman ga mutane da ke fama da cutar numfashi ta asthma".

"Irin wannnan yanayi lokaci ne da ba ya masu daɗi."

Farfesan ya ba da shawarar cewa iyaye su kiyaye irin suturan da ake sanya wa ƙananan yara, tare kuma da ciyar da su abinci mai gina jiki domin kare su daga haɗurran da ke tattare da lokacin sanyi.

No comments