Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Advertisement

 


Breaking News:

latest

ZAMFARA: A Wata Mai Zuwa Jirgin Sama Zai Fara Jigilar Fasinjoji Tsakanin Gusau Da Abuja

Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanya hannu kan yarjejeniyar haÉ—in gwiwa da kamfanin XEJet Limited domin fara zirga-zirgar jiragen fa...

Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanya hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa da kamfanin XEJet Limited domin fara zirga-zirgar jiragen fasinja kai tsaye tsakanin Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Gusau da Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Yarjejeniyar Fahimtar Juna, wato MoU da aka sanya wa hannu ranar Litinin ta zama wani muhimmin mataki wajen inganta zirga-zirgar jama’a da kuma sauÆ™aÆ™a harkokin kasuwanci, zuba jari, yawon buÉ—e ido da bunÆ™asar tattalin arzikin Jihar Zamfara.

Wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa Mataimakin Gwamnan jihar, Malam Mani Mummuni, ne ya jagoranci bikin sanya hannu kan yarjejeniyar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Abubakar Mohammed Nakwada, ne ya sanya hannu a madadin gwamnatin jihar.

Sanarwar ta ce, “Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanya hannu kan Yarjejeniyar Fahimtar Juna (MoU) da kamfanin XEJet Limited kan bunÆ™asa hanyar zirga-zirgar jiragen sama, domin fara zirga-zirgar jiragen fasinja tsakanin Abuja da Gusau.

“ƘarÆ™ashin yarjejeniyar, XEJet zai fara zirga-zirgar jirage sau biyu a kowane mako daga wata mai zuwa.

“Sabuwar hanyar zirga-zirgar jiragen sama za ta inganta damar zuwa Zamfara tare da buÉ—e Æ™arin damammaki ga masu zuba jari, ’yan kasuwa da baÆ™i.”

Da yake jawabi a wajen bikin, Mataimakin Gwamna Mani Mummuni ya ce haÉ—in gwiwar ya yi daidai da manufar gwamnatin jihar ta inganta ababen more rayuwa na sufuri.

Ya ce, “An gina Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Gusau ne tun daga tushe, kuma aka kammala shi cikin shekaru biyu.

“Babbar manufar gina filin jirgin shi ne sauÆ™aÆ™a tare da inganta zirga-zirgar mutane da kayayyaki, abin da zai taimaka wajen bunÆ™asa tattalin arzikin jihar.

“Gwamna Lawal yana ci gaba da neman masu zuba jari na Æ™asa da Æ™asa da hukumomin bayar da tallafi, waÉ—anda dukkansu suke da niyyar zuba jari a Zamfara.

“Wannan matakin fara zirga-zirgar jiragen kasuwanci zai jawo hankalin masu zuba jari. Inganta damar isa jihar ita ce babbar manufarmu, domin hakan zai samar da yanayi mai kyau ga bunÆ™asar kasuwanci da zuba jari.”

No comments