Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Zan Dawo Da Martabar Jihar Zamfara A Idon Duniya -Gwamna Lawal

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya Ζ™ara jaddada aniyar sa ta sake gina Zamfara don dawo da matsayin ta na dandalin kasuwanci a...

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya Ζ™ara jaddada aniyar sa ta sake gina Zamfara don dawo da matsayin ta na dandalin kasuwanci a Arewacin Nijeriya. 

Gwamnan ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin gudanar da bikin Ζ™addamar da fara ginin tashar tashi da saukan jiragen sama, wanda Ministan harkokin Sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya Ζ™addamar jiya a Gusau. 
A cikin wata sanarwa da Kakakin Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu jiya, ta bayyana cewa filin jiragen saman da ke Gusau da za a gina, zai zama wani ingantaccen wuri ne da za a rinΖ™a hidimar harkar jiragen Ζ™asar nan da na Ζ™asashen waje.

Kakakin Gwamnan ya Ζ™ara haske da cewa, wannan aiki zai haΙ—a da gina layin tashin jirage mai kilomita 3.4 don jirage masu zirga-zirga, sanya fitilu a layin, da sauran na'urorin da ke taimaka wa tashi da sauran jirage. 

Wani Ι“angare na jawabin Gwamna Lawal, ya Ζ™ara jaddada cewa gwamnatin sa ta duΖ™ufa wajen tabbatar da jihar Zamfara ta shiga fagen gogayya a harkokin kasuwanci, wanda zai jawo hankalin masu zuba jari daga ciki da wajen Ζ™asar nan. 

Ya ce, “Mai girma Minista, manyan baΖ™i, maza da mata, 'yan jarida, wannan tashar jirgin saman za ta Ζ™unshi wurin tashin jirage irin na zamani da yanayi mai kyau ga fasinjoji, wanda zai haΙ—a da wurin tantancewa, wurin duba jakunkuna irin na zamani, wuraren jira, da kuma wuraren jami'an Kwastam da na shige da fice. Bugu da Ζ™ari, tashar nan za ta samu ingantaccen sashen kula da hada-hadar jirage, wanda zai Ζ™unshi na'urorin sadarwa irin na zamani. 
“Haka kuma, wurin zai Ζ™unshi gina sashen kula da gyare-gyare, sashen kashe gobara da ceto, wurin ajiyar man jirgi, hanyoyin zuwa tashar jirgin, wuraren ajiye ababen hawa ga fasinjoji da ma'aikata, samar da isasshe kuma ingantaccen ruwa, isasshiyar wutar lantarki da na'urorin sadarwa.

“Wannan tashar jirgin sama ta Gusau, tsararre ne da zai Ζ™unshi duk wani fanni na tashi da saukar jirage daga sassan Ζ™asar nan da na Ζ™asashen waje, zai zama wata mahaΙ—a ta yankin. Kowane irin jirgi zai iya sauka a wurin, zai samar da sassauΖ™ar hanyar shiga da fita jihar Zamfara, tare da inganta mu'amala, kasuwanci da yawon buΙ—e ido.

"Kamfanin gine-gine na 'Triacta Nigeria Limited' ne zai gudanar da aikin, bisa shawarar kamfanin 'JBI Tech Consult', bisa yarjejeniyar kammala aikin a tsakanin watanni 30.

“Akwai amfani mai yawa da ke Ζ™unshe a harkar gina wannan tashar jirgi ta Gusau, musamman a fannin tattalin arziki, domin zai samar da hanyoyin samun kuΙ—aΙ—en shiga da kuma inganta zamantakewa da alaΖ™a da jihar Zamfara. Zai samar da hanyar shiga jihar mu kai tsaye ta jiragen sama, wanda zai kawar da wahalhalun da 'yan kasuwa ke sha wajen jigilar hajojin su.”

Tun farko a nasa jawabin, Ministan sufurin jiragen sama na Ζ™asar nan, Festus Keyamo ya bayyana cewa Zamfara ta kasance koma-baya a harkokin ci gaba, a daidai lokacin da sauran jihohin yankin Arewa maso Yamma su ke da ingantattun filayen jiragen sama, amma ita ba ta da shi, duk da kasancewar ta cibiyar noma a yankin. 

Ministan ya ce, "Amma dai ba a makara ba. Wani Ι—an jarida daga Ζ™asar waje ya kira ni yana tambaya ta ko Zamfara na buΖ™atar tashar jirgin sama. Ina da yaΖ™inin cewa samar da tashar jiragen sama a Zamfara, ba wai ga haΙ“aΙ“aka karkar kasuwanci kawai ya tsaya ba, zai inganta harkar walwala da jin daΙ—in jama'a. Bisa abubuwan da na lura da su, lallai jihar a shirye ta ke wajen wannan ci gaba.

"Ina so in dawo nan a shekara mai zuwa don Ζ™addamar da jigilar maniyyata aikin Hajji. Maniyyatan jihar Zamfara sun kwashe shekaru dama suna shan wahala wajen hawa jirgi zuwa Ζ™asa mai tsarki. Wannan ba zai sake faruwa ba. Don haka ina tabbatar wa da Ι—an uwana, Gwamna Dauda Lawal cewa, ina bayan ka, ina tare da kai, ina tare da al'ummar jihar Zamfara don ganin wannan mafarki ya zama gaskiya.

No comments