Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Zamfara Kan Gaba A Jarabawar NECO Ta Bana

Jihar Zamfara ta zama jihar da ta fi kowace jiha a Arewacin Nijeriya, kuma ta zamo ta biyu a faÉ—in Nijeriya a jarrabawar da Huku...

Jihar Zamfara ta zama jihar da ta fi kowace jiha a Arewacin Nijeriya, kuma ta zamo ta biyu a faÉ—in Nijeriya a jarrabawar da Hukumar Jarrabawa ta Ƙasa (NECO), ta ke shirya wa É—alibai ’yan baiwa a Nijeriya.

A makon da ya gabata ne Hukumar shirya jarabawar ta ƙasa ta fitar da Sakamakon Ɗalibai Masu Hazaƙa na 2024 don shiga Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Suleja.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar a ranar Lahadi, ya ce jihar Zamfara ce ta samu mafi yawan gurbi, inda ta zama jihar da ta yi fice a faÉ—in Arewa.

Ya ƙara da cewa, a faɗin ƙasar nan Zamfara ta zo ta biyu da haziƙan ɗalibai 30, yayin a jihar Anambra ta samu matsayi na ɗaya da ɗalibai 35.

“ÆŠaliban Jihar Zamfara sun samu mafi girman maki a jarabawar NECO na É—alibai masu hazaÆ™a a cikin jihohin Arewa 19, wanda hakan ya haifar da wani gagarumin ci gaba a É“angaren ilimin jihar.

“A karon farko jihar Zamfara ta yi fice a matakin Æ™asa, wanda ke nuna gagarumin sauyi daga matsayin da ta saba samu.

“NECO tana shirya jarabawar yara haziÆ™ai da 'yan baiwa domin samun gurbin karatu a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Suleja. ’Yan makarantar Firamare na shekarar Æ™arshe ne kawai kuma 'yan Æ™asa da shekara 11 za su iya rubuta jarabawar, a Disambar shekarar jarabawar.”

Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Suleja, makaranta ce da ake horar da yara ’yan baiwa da masu hazaÆ™a a Nijeriya. Tana Æ™ara buÉ—e damarmaki ga É—alibai 'yan baiwa don haÉ“aka iyawarsu cikin sha'awar gina Æ™asa da ci gaban fasaha.

ÆŠaliban za su amfana da tallafin karatu na Gwamnatin Tarayya ta hanyar koyarwa, kuÉ—aÉ—en jarrabawa, wurin kwana, ciyarwa, kayan makaranta da litattafai.

“A shekarar 2024, Zamfara ta samu gurbi uku bisa Æ™a’ida ta jiha kuma ta samu Æ™arin gurbi 27 bisa la’akari da cancantar matsayinta a cikin tattalin arzikin Gwamnatin Tarayya. ÆŠaliban Zamfara sun yi fice a jarrabawar, inda suka samu gurbi fiye da kowace jiha a Arewa.

“Wannan babban ci gaba ne, musamman idan aka yi la’akari da cewa an kafa dokar ta-É“aci a fannin ilimi a jihar a bara.

“A cikin yara 30 masu hazaÆ™a daga Zamfara, 21 mata ne, 9 kuma maza ne, wanda hakan ke nuni da yadda ake Æ™ara Æ™arfafa ilimin 'ya’ya mata a jihar.

“Gwamnatin Jihar Zamfara za ta ci gaba da yin Æ™oÆ™ari wajen ganin an aiwatar da cikakken manufofin ilimi, wanda hakan zai sa a samu Æ™arin nasarori ga jihar.”

No comments