Daga Ibrahim Muhammad Rundunar 'yan sanda shiyya ta ɗaya da ke kula da jihar kano da Jigawa ta buƙaci al'umma su yi wa...
Daga Ibrahim Muhammad
Rundunar 'yan sanda shiyya ta ɗaya da ke kula da jihar kano da Jigawa ta buƙaci al'umma su yi watsi da wani rahoto da ke cewa ta yi wa umarnin kotu karan tsaye.
Rundunar a cikin wata sanarwa da kakakinta, CSP Bashir Muhammd ya fitar aka raba wa manema labarai ta ce, tun da fari sun karɓi wani ƙorafi daga wani mutum mai suna Alhaji Abdullahi Sharaɗa wanda ya yi zargin cewa wani mutum mai suna Alhaji Ɗayyabu da wasu mutane uku sun zambace shi kuɗi N50,000,000.
Mai ƙorafin ya ce an yi masa tallan wani gida ne kuma ya tura kuɗin, amma sai ya fahimci akwai yaudara a cinikin, don haka sai ya buƙaci a dawo masa da kuɗinsa, amma hakan ya gagara.
Shi ne ya shigar da ƙorafi ga rundunar 'yan sandan shiyya ta ɗaya, kuma ya buƙaci a dawo masa da kuɗin da ya tura tun da fari.
A sanarwar da rundunar ta fitar ta ce, domin faɗaɗa bincike wajibi ta gayyaci dukkan waɗanda ke cikin wannan dambarwa domin gano bakin zaren.
Bayan bincike sun gano wani asusu na Bankin Zenith 1012679910 da ke ƙarƙashin kulawar kotu, tare da gano asusun ajiya biyu da aka tura wani adadi na kuɗaɗen a ciki.
Sai dai asusu guda biyu da aka gano N10,000,000 ba asusun ajiyar kotun bane wanda ya zama wajibi su gudanar da bincike domin gano gaskiya.
Magatakardar kotun shari'ar Musulunci da ke kasuwa, wanda yana da masaniya game da yadda aka tura wannnan kuɗi ya ce yana aiki ne bisa umarnin Mai Shari'a Abdu Abdullahi Wayya.
Kuma domin samun cikakken bayani da gano gaskiya a kan wannan batu dole sai sun samu bayani daga kowane ɓangare da ke da alhaki a kan wannan batu.
"Don haka muna gudanar da bincike ne a kan zargin aikata laifin zamba cikin aminci, wanda kuma babbar kotun tarayya da ta jiha ne kaɗai ke da hurumim dakatar da mu kamar yadda sashi 46 na kundin tsarin mulkin ƙasar nan ya yi tanadi," in ji sanarwar.
CSP Bashir Muhammad buƙaci kafafafen yaɗa labarai su riƙa tabbatar da abu kafin wallafawa, tare da tuntuɓar waɗanda lamarin ya shafa domin sanin haƙiƙanin gaskiya a kan duk wani abu da ya taso.
No comments