Daga Muhammad Sakafa A a karshen makon nan ne, ’yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky suka gudanar da gagarumin biki...
Daga Muhammad Sakafa
A a karshen makon nan ne, ’yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky suka gudanar da gagarumin bikin yaye mahaddata Alkur’ani mai tsarki karo na 14 a filin masallacin Juma’a da ke kofar fadar Sarkin Kano.
Taron ya samu halartar dubban jama’a maza da mata da suka fito daga makarantun Fudiyya daban-daban da sauran makaratun haddar Alkur’ani da ake da su a duk fadin kasar nan.
Alarammomi da gwanayen Alkur’ani ne suka gwada haddar da kuma yi masu darasu. Daliban sun kai 186 an raba su rukuni-rukuni. Ana jawo masu Alkur’ani daga bangarori daban-daban suna cafka suna ci gaba da karantawa.
A jawabinsa da aka saurara a taron, Jagora, Shaikh Ibraheem Zakzaky, ya jawo hankalin daliban a kan sanin muhimmancin abin da suke yi. Ya bukaci su tabbatar sun rike haddar da suka yi, sannan kuma su san ma’anar Alkur’ani. “Rike hadda, don ita hadda idan aka yi aka bar ta tana tafiya ne (za ta tafi abinta), don ko ka yi haddar in dai ba ka yin karatu, wata rana kana cikin yi sai ka ga wani wuri ya cije maka. Mumini bai karanta Alkur’ani ko sau daya a shekara ba, to Alkur’anin zai iya kai shi kara (wajen Allah), wannan ya ci zarafin Alkur’ani, ya masa jafa’i,” in ji shi.
Wakilin ’yan’uwa na Kano, Dakta Sunusi Abdulkadir Kano, ya yi jinjina ta musamman ga Jagora Shaikh Zakzaky, inda ya bayyana cewa duk wadanda suka haddace Alkur’ani aikin sa suke yi. “Duk wanda ya haddace ko da Aya daya ne ta Alkur’ani a Fudiyya, to aikin Allama Zakzaky ne, saboda shi Malamin ai aikin Malam Zakzaky yake yi. Muna kara jinjina ga Allama Sayyid Ibraheem Zakzaky,” in ji shi.
Ya yi wa daliban albishir da cewa daga wannan shekarar duk wanda ya haddace Alkur’ani da shi za a je wajen ganawa da Jagora. “Su Allama sun ce shekara mai zuwa duk dalibin da ya haddace Alkur’ani da shi za a gana da Malam. Sawa’un daliban nan sun kai 50, sun kai 100, sun kai 150, ko dari nawa ne. Su Malam sun ce suna son su ga mahaddata din a shekara mai zuwa,” ya jaddada.
Malam Muhammadu Kamaluddeen, Mahaifin Fatima, daya daga cikin daliban da suka haddace AlKur’ani, amma sai ta rasu kafin wannan ranar, ya bayyana wa manema labarai a wajen taron cewa, “Duk abin da Allah ya hukunta babu yadda muka iya, amma mun ci burin ya kasance ina tare da Fatima a daidai wannan ranar.”
A lokacin da yake zantawa da manema labarai, daya daga cikin masu shirya taron, Shaikh Imam Kurna, ya bayyana taron a matsayin wani dandamali da ke hada dukkan a’'ummar Musulmi, saboda taro ne na Alkur’ani. “Taro ne wanda ya hada dukkan al’ummar Musulmi saboda taro ne na Alkur’ani. Musulmi daga bangarori daban-daban sun halarta. Ya yi fatan Allah ya amfanar da mu da abin da ke cikin Alkur’ani. Abin da ya shafi Alkur’ani, wani abu da ya shafi Musulunci gaba daya.
“Ya ja hankalin wadanda aka yaye din a kan yin riko da karantawar Alkur’ani da yin aiki da shi. Ya kamata al’ummar nan su fahimci shi fa Alkur’anin nan Allah ya aiko da shi ne don ya zama tsari na rayuwarmu, wanda ya kunshi dokoki da shugabanci na Musulunci,” ya bayyana.
Wakilin ’yan’uwa na Gombe, Shaikh Muhammad Abbari, ya bayyana matukur jin dadinsa da ganin wannan ranar, musamman yadda ya ga yara suna karanta Alkur’ani gaba gadi ba tare da wata fargaba ba. “Duk abin da mutum yake zai so ya bar baya. Wadannan yaran da aka dora su a kan haddar Alkur’ani ba karamin abin farin ciki ba ne. Muna so mu ga ’ya’yanmu sun san Alkur’ani, ba kawai don su san babbaku da farfaru ba, kuma ba saukar zuku ba, hafizai ne ake tarawa maza da mata.
Shi kuwa daya daga cikin ’yan kwamitin shirya taron, Malam Ibrahim Badawa kira ya yi ga dukkan ’yan’uwa su taimaka wajen ganin dorewar wannan tsarin. “Ina kira ga ’yan’uwa baki daya su yi musharaka wajen ba da gudunmawa don ganin an inganta wannan tsarin.
“Tun lokacin da Shahid Muhammadu Turi ya zo wannan gari ya tsara wani tsari, ta yadda lokacin da yaro zai gama Firamare ya kammala haddar Alkur’ani, ta yadda zai zama duk shekara za a rika yaye mahaddata a dukkan fadin kasar nan, ta yadda zai zama nan da shekara da shekaru Harkar Musulunci zai zama tana da dubban mahaddata”, in ji shi.
Shaikh Sharif Ali Murtada Fagge shi ne hedimastan Fudiyya Rijiyar Lemo, ya tabbatar mana da cewa, babban hadafinsu a nan gaba shi ne ya zama sun samar da Mahaddaci kuma Injiniya a lokaci guda. “Hadafinmu a kan wadannan yaran shi ne ya zama Hafizan Alkur’ani, kuma suna da ilimin zamani. Ya zama Hafizin Kur’ani kuma Injiniya. Irin wadannan yaran ne suke ake kira ’ya’yanmu jarinmu. Sune za su zama shugabannin a nan gaba, wadanda za su yi abin da Allah (T) yake so a bayan kasa,” ya bayyana.
Ya yi kira ga iyaye su rika kula da ’ya’yansu yadda ya kamata. “Bayan an haddace Alkur’ani sai ya zama an kiyaye shi, kuma a yi aiki da shi. Su kuma iyaye su sani bayan dansu ya haddace Alkur’ani, kar su sake shi haka sakaka, har yanzu yana kan wuyanka, sai ka kula masa da Alkur’anin nan da ya haddace, kai za ka tsare masa shi, har ya zuwa ya girma ya zama mukhallaf.”
Fatima Aminu daga Fudiyya Falgoren Daji, wacce ta samu wata baiwa ta kiyaye wasu surori da ayoyi a cikin Alkur’ani, ta bayyana mana matukar farin cikinta da wannan nasara da ta samu ta haddace Alkur’ani a wannan shekarar. “Gaskiya ina jin farin ciki da ban taba jin irin sa ba a rayuwata.
“Bayan na gama haddar Alkur’ani sai na biyo cikin Alkur’anin ina tantancewa da bincikawa tun daga Bakara har Nasi ina tanatance Zalikan da ke cikin Alkur’ani. Na bambance Zalikan da ke cikin Alkur’ani, inda na gano 277 ne. Sannan kuma na tantance ‘Ya Ayyuhallazina Amanu!’ Na gano 89 ne.”
Shi ma Aliyu Ibrahim daga Fudiyya Darazo, daya daga cikin daliban da suka haddace Alkur’ani, wanda kuma yake da baiwar sanin surori, ayoyi da shafukan Alkur’ani, ya bayyana matukar jin dadinsa da Allah ya nuna masu wannan ranar. “Iyaye suna tsayawa yara, amma mu dai Malam Aliyu Yusuf Zariya ne ya tsaya mana tsayin daka, don mu yi karatu yadda ya kamata,” ya tabbatar.
Malam Muhammad Kamilu Salisu, daya daga cikin ’yan Dandalin Mahaddatan Alkur’ani na Harkar Musulunci, ya shaida mana hanyoyin da suka bi wajen tantance mahaddatan da aka samu a wannan shekarar da kuma yadda aka yi suka gano wasu haddatar tasu tana da kwari, wasu kuma tana da rauni, abin da ya sa suka bukaci a jinkirta masu zuwa shekara mai zuwa.
“Muna tattarawa da tantance wadannan daliban ne ta hanyar yi zagaye na akalla wata uku. Duk garin da muka san akwai makarantar Tahfiz, sai mu je mu tantance daliban da suka haddace Alkur’ani, sai mu dawo mu tattara adadin. Ina son daliban nan su gane, ko da ba ka zama Mahaddaci a wannan karon ba, kar tunaninka ya rika ba ka ba za ka iya ba. Kowane lokaci in ka mai da hankali za ka iya.”
Malam Muhammad Awwal Sa’id shi ne shugaban kwamitin iyayen yara na makarantun Fudiyya, “Lallai yau ina cikin farin ciki. Alhadullahi an samu nasarori. Nasarar da muka samu a wannan taron ta fi akasin da aka samu. Insha Allah a shekarar mai zuwa za mu sake dubawa don mu gyara duk wata matsala da aka samu a wannan shekarar.”
Malam Muhammad Awwal, wanda shi ne Hafizi ne da ya rubuta Alkur’ani har guda shida da hannunsa, ya yi kira ga daliban da su sake zage damtse wajen ganin sun cimma burinsu na haddar Alkur’ani. Hakan ne za isa hakarsu ta cimma ruwa.
Ya yi amfani da wannan damar inda ya mika godiyarsa ga mahalarta taron da kuma duk wadanda suka taimaka ta kowane janibi wajen ganin taron ya samu nasarar da ya samu.
Kafin a raba takardun shaida ga daliban da suka nuna kwazo, Shaikh Musbahu Yusuf Makwarari, ya nuna matukar jin dadinsa, tare da yaba kokarin da Harkar Musulunci ke yi wajen karfafa haddace Kur'ani mai girma tun suna yara kanana.
No comments