Gwamnatin jihar Zamfara ta ƙaryata wani labari da ke ikirarin cewa wata Musulma da ta zama Kirista a jihar, Zainab, za ta gurfan...
Gwamnatin jihar Zamfara ta Ć™aryata wani labari da ke ikirarin cewa wata Musulma da ta zama Kirista a jihar, Zainab, za ta gurfana a gaban Kotun Shari’ar Musulunci a ranar Juma’a saboda ta sauya addini.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa rahoton tsantsagwaron ƙarya ne kuma an ɗauko shi ne daga shafukan sada zumunta da ke neman janyo cece-ku-ce.
Sanarwar ta Ć™ara da cewa, babu shakka an tabbatar da cewa babu irin wannan shari’a a gaban wata kotun shari’a a jihar Zamfara.
“An jawo hankalin gwamnatin jihar Zamfara kan munanan labaran Ć™arya da ke yawo a kan wata mata mai suna Zainab Muhamadu ‘yar shekara 22, wacce ke fuskantar hukuncin kisa saboda ta shiga addinin Kirista.
“Muna so mu bayyana cewa aikin maĆ™iya zaman lafiya ne, waÉ—anda suke neman hanyar haifar da tashin hankali a inda ake zaman lafiya.
“Labarin Ć™aryar, wanda wani dandali na yanar gizo da ya yi Ć™aurin suna wajen yaÉ—a labaran bogi ya yaÉ—a, ba wani abu ba ne illa yunĆ™urin dagula zaman lafiya da ba za a yi nasara ba.
“Gwamnatin jihar Zamfara ta yi gaggawar É—aukar matakin gayyato dukkan hukumomin da abin ya shafa da jami’an tsaro domin tabbatar da sahihancin labarin, wanda a Ć™arshe ta gano cewa Ć™arya ce kawai da Sahara Reporters ta Ć™irĆ™ira.
“Don tabbatar da gaskiya, gwamnatin jihar ta tuntubi Babban AlĆ™ali na Kotun Shari’ar Musulunci a Zamfara dangane da irin wannan shari’a, inda ya bayyana cewa ba a taba samun irin wannan Ć™ara a gaban wata kotun shari’a a jihar Zamfara ba.
"Tambayar ita ce, daga ina ne wannan labari mai cike da haÉ—ari da raba kan jama'a ya samo asali? Mene ne dalilin yaÉ—a shi? Mene ne masu yaÉ—a wannan labari suke fatan cimmawa a nan gaba?
"Muna rayuwa ne a cikin lokuta masu ban sha'awa. Kafofin watsa labarai da ya kamata su samar wa jama'a da ingantattun labarun suna zama abin kunya, sun zama masu kwafa da watsa labaran bogi don samun mabiya da 'likes'.
“Matar da aka yi amfani da hotonta wajen yaÉ—a labaran bogi ba ‘yar Nijeriya ba ce, sunanta Aalia, kuma ‘yar jihar Texas ce ta Ć™asar Amurka.
“Gwamnatin jihar Zamfara ta yi imanin cewa ya zama dole ta fayyace cewa babu wani abu makamancin haka da ke faruwa a jihar.
"Muna kira ga jami'an tsaro da abin ya shafa da su binciki tushen wannan labari na bogi, ba gaskiya ba ne, wanda ke neman haifar da tashin hankali na addini, tare da gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a gaban kotu, dole ne mu ba da gudubmawar mu don tabbatar da zaman lafiya a ƙasar nan."
No comments