Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

AYYUKAN RAYA ƘASA: Sanata Orji Kalu Ya Jinjina Wa Hazaƙar Gwamna Lawal

Sanata Orji Uzo Kalu, tsohon gwamnan jihar Abia, ya yaba wa gwamnatin Gwamna Dauda Lawal kan sauya fasalin jihar Zamfara. A rana...

Sanata Orji Uzo Kalu, tsohon gwamnan jihar Abia, ya yaba wa gwamnatin Gwamna Dauda Lawal kan sauya fasalin jihar Zamfara.

A ranar Litinin da ta gabata ne Sanata Kalu ya ƙaddamar da ginin Ma’aikatar Harkokin Mata da Ci Gaban Jama’a ta Jihar Zamfara da aka sake ginawa da kuma sabon ginin Kwalejin Fasaha da Kimiya ta Jihar Zamfara (ZACAS).

Wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa a baya ma’aikatar tana gudanar da ayyukanta ne daga wani ɗan ƙaramin gini wanda bai isan ma'aikatanta, kuma bai dace da muhimman ayyukan da ma’aikatar ke gudanarwa ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa, ta hanyar tsare-tsare na hangen nesa da aiwatar da ayyuka, Gwamna Lawal ya mayar da wannan ƙaramin gini zuwa katafaren gini na zamani, mai rukunai da dama, kuma mai hawa biyu.

A yayin ƙaddamar da ginin ma’aikatar harkokin mata, Gwamna Lawal ya bayyana cewa, wannan tsari mai ban sha’awa na nuni da muhimmancin rawar da ma’aikatar ta ke takawa wajen ayyukan ceto da ci gaban gwamnatinsa.

“Ina mai matuƙar godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki da ya ba ni kwarjinin gudanar da aikin kuma ya nufe ni, na tsaya a gabanku a yau domin na ƙaddamar da wannan sabon gini da aka gina na Ma’aikatar Harkokin Mata da Ci Gaban jama’a ta Jihar Zamfara, da kuma aza harsashin ginin sabuwar cibiyar mata a wannan harabar.

“Haka kuma ina farin cikin yi wa babban baƙonmu na musamman, abokina kuma abokin Jihar Zamfara, ɗan uwana, Babban Sanatan Tarayya, Sanata Orji Uzor Kalu barka da zuwa.

“Wannan taron da muka kasance a nan a yau ba wai kawai don ƙaddamar da gibi ba ne kawai, amma; yana nufin sake tabbatar da ɗorewar gwamnatinmu na sabunta cibiyoyi, ci gaban al'umma, da gudanar da mulki baki ɗaya.

"Yana nuna cewa kare mutunci da jin daɗin matanmu, yara, masu nakasa, da masu rauni shi ne jigon falsafar mulkinmu."

A lokacin da yake ƙaddamar da sabbin gine-ginen da aka gyara tare da inganta su a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Zamfara (ZACAS), Gusau, Gwamna Lawal ya jaddada cewa taron ya nuna wani gagarumin ci gaba a yunƙurin gwamnatinsa na sake farfaɗo da ilimi a matsayin ginshiƙin ci gaba da wadata a jihar Zamfara.

“Tsarin da muka ƙaddamar yana nuni da shirin da aka yi a tsanake da kuma aiwatar da shi don mayar da ZACAS zuwa wata cibiya mai aiki, samar da gasa, da kuma janyo ɗalibai a jiki, biyo bayan duk matakan da suka dace na bayar da kwangilar, an bayar da aikin gyaran ne ga kamfanin Bankanu & Partners Limited, wanda kwararren kamfani ne mai bin ƙa'idojin aiki kuma cikin inganci inda muke iya ganin sakamakon a gabanmu.

“A kashi na farko da na biyu na aikin, mun gudanar da gyaran gaba ɗaya na muhimman cibiyoyin ilimi waɗanda suka daɗe a lalace kuma ba su da tasiri wajen koyo da koyarwa.

“Haka zalika, an gyara ɗakin karatu na kwalejin, inda aka samar da fili mai inganci da wadatuwa don gudanar da bincike a fannin ilimi. Daya daga cikin muhimman kadarorin wannan cibiyar shi ne ɗakin taro na Sardauna mai kujeru 200, shi ma an gyara shi tare da zamanantar da shi.

"Ɗakin Mass Communication Studio and Theater, da Cibiyar Kwamfuta (CBT) duk an gyara su gaba ɗaya. An canja fasalin ɗakin taron Yusuf Anka don ɗaukar ayyukan ilimi da zamantakewa. A halin yanzu, manyan ɗakunan gwaje-gwaje na kimiyya guda uku - Biology, Chemistry, da Physics - an sabunta su gaba ɗaya don tallafawa ingantaccen ilimin kimiyya da gwaje-gwaje.

“Ɗaya daga cikin abubuwa masu matuƙar muhimmanci shi ne gyaran ɗakunan ɗalibai, wanda ke da matuƙar muhimmanci ga walwala da jin daɗin ɗalibai, an gyara ɗakin ɗalibai mata ɗaya da ɗakunan ɗalibai maza uku domin inganta rayuwa da kuma ɗaukaka darajar ɗalibai.”

Tun da farko, Sanata Kalu ya yaba da ƙoƙarin Gwamna Dauda Lawal, musamman nagartar ayyuka a ma'aikatar mata ta jihar Zamfara da kuma kwalejin fasaha da kimiya ta jihar Zamfara.

Ya bayyana cewa abin da ya gani a Zamfara kawo sauyi ne, inda gwamnan ke samun cikakken goyon bayan al’ummarsa.

No comments