Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Ban Ciwo Bashin Ko Kwabo Ba Don Gyara Jihar Zamfara -Gwamna Lawal

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana cewa gwamnatinsa ba ta karbi lamuni ko rance domin gudanar da ayyukan kawo sauyi d...

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana cewa gwamnatinsa ba ta karbi lamuni ko rance domin gudanar da ayyukan kawo sauyi da ake yi a duk faÉ—in jihar ba, kuma duk da haka yana da isassun kuÉ—i a ausun jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawa da ya yi da wasu Editoci a ofishin sa da ke Gusau, babban birnin jihar a ranar Laraba, inda ya yi cikakken bayani kan nasarorin da gwamnatin sa ta samu tun hawan sa mulki kusan shekaru biyu da suka gabata.

Gwamna Lawal ya bayyana manyan ci gaban da aka samu a bangarori masu muhimmanci da suka haɗa da tsaro, ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa, da ƙarfafa tattalin arziki.

Ya nanata cewa nasarar da aka samu ya zuwa yanzu ta samo asali ne sakamakon kyawawan tsare-tsare, ingantaccen jagoranci, da kuma kula da albarkatu.

Gwamnan ya bayyana cewa an samu ci gaba sosai a harkar tsaro a jihar idan aka kwatanta da abin da ya gada a shekarar 2023.

A cewar sa, inganta haÉ—in gwiwa da jami’an tsaro ya taka muhimmiyar rawa wajen rage yawaitar ayyukan ‘yan bindiga da sauran miyagun ayyuka a Zamfara.

Dangane da ababen more rayuwa kuwa, Gwamna Lawal ya ba da misali da ayyukan da ake ci gaba da aiwatarwa da kuma waÉ—anda aka kammala a Æ™arÆ™ashin shirin “Renewal Project,” wanda ya haÉ—a da gine-gine da gyaran hanyoyi, makarantu, da cibiyoyin kiwon lafiya a dukkanin Æ™ananan hukumomi goma sha huÉ—u na jihar.

Gwamna Lawal ya kuma bayyana shirin gwamnatin sa na bunÆ™asa fannin haÆ™ar ma’adanai, inda ya bayyana shi a matsayin wani muhimmin fanni na bunÆ™asar tattalin arziki da ake samu a yanzu da aka samu daidaiton tsaro a jihar.

Da yake jaddada Æ™udirin gwamnatin sa na tabbatar da gaskiya da riÆ™on amana da kuma tafiyar ci gaban al’umma, Gwamna Lawal ya nanata cewa duk nasarorin da aka samu ya zuwa yanzu an cimmasu ne ba tare da karbar rancen ko kobo É—aya ba.

Ya kuma tabbatar wa da al'ummar jihar Zamfara cewa akwai wasu ayyukan ci gaba a nan gaba, domin gwamnatin sa ta ci gaba da mayar da hankali wajen ganin an samar da ci gaba mai É—orewa da inganta rayuwar al’umma a faÉ—in jihar.

Da ya ke amsa tambaya dangane da rikicin PDP, Gwamna Lawal ya yi imanin cewa rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP ya wuce É—an takarar ta na shugaban Æ™asa a zaben 2023, Atiku Abubakar, kuma ya samo asali ne daga faÉ—an son rai a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar.

“Kowa yana da nasa batun; ba wai batun Atiku Abubakar ba ne, ya wuce shi,” inji shi.

"Matsala ce ta cikin gida a cikin PDP, kuma muna yin ƙoƙari sosai. Ina ganin abin ya shafi kishin mutane ne, kowa da kowa."

No comments