Tsohon shugaban ƙasar nan, Chief Olusegun Obasanjo zai shiga jihar Zamfara domin ƙaddamar da wasu ayyukan da Gwamna Dauda Lawal ...
Tsohon shugaban ƙasar nan, Chief Olusegun Obasanjo zai shiga jihar Zamfara domin ƙaddamar da wasu ayyukan da Gwamna Dauda Lawal ya yi a jihar, wanda zai haɗa da babban asibitin Yariman Bakura da kuma wasu hanyoyi a babban birnin jihar.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar a Gusau yau ɗin nan, ya bayyana cewa a gobe Talara 17 ga wannan wata na Yunin 2015 ne tsohon shugaban ƙasar zai gudanar da waɗannan ayyuka.
Sulaiman Bala ya ƙara da cewa wannan asibiti da Obasanjo zai buɗe, asibiti ne da aka yi wa ingantaccen gyara, tare da wadata shi da kayan aiki irin na zamani.
"Haka kuma, tsohon shugaban ƙasa Obasanjo zai ƙaddamar da wasu tituna a Unguwar GRA ta Guasau, wacce ta kasance ɗaya daga cikin ayyukan da gwamnan ya aiwatar a shirin gwamnatin sa na sake inganta biranen jihar," in ji sanarwar.
No comments