Daga Ibrahim Muhammad An bayyana damuwa game da yadda aikin Lauya a ƙasar nan ke fuskantar ƙalubale sakamakon akwai shari'u...
Daga Ibrahim Muhammad
An bayyana damuwa game da yadda aikin Lauya a ƙasar nan ke fuskantar ƙalubale sakamakon akwai shari'u da dama da Kotun Ƙoli da yanke hukunci a kan damar da hukumomi masu yaƙi da cin hanci rashawa, musamman ma waɗanda suka shafi jahohi suke da shi, amma duk da haka wasu lauyiyi na cigaba da kai ƙararraki a gaban kotu na ƙasa bayan sun san Kotun Ƙoli ta yanke hukunci a kai.
Shugaban Hukumar ICPC, Dakta Musa Adamu Aliyu ne ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi a yayin taron ƙaddamar da mujallar BAR VOICE da ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa reshen Ungogo jihar Kano ta wallafa a ranar Asabar.
Ya ja hankalin lauyoyi su kiyayi yin duk abin da bai kamata ba da zai jawo rage kimar aikin, musammann
yanzu da ake zamani na aiki da fasahar zamani da za a iya ɗaukar kowane Lauya a auna shi a mizani daga yadda yake kare takardunsa da abubuwa da yake faɗa. "Irin wannan na'ura ta fasahar zamani za ta iya gaya maka daga abubuwan da yake a takardunsa a gaban kotu. Lauya ne mara gaskiya wanda ba ƙoƙari yake ya kare gaskiya ba, duk za a gane," in ji shi.
Ya ja hankalin lauyoyi da cewa idan suna yin wani abu da bai dace ba wata rana za a iya ɗauko Lauya a sa shi a mizani a ce daga takardun da yake kai wa kotu ya nuna cewa akwai matsala a tare da shi, ya kamata a kalli wannan abu don a kiyaye a tsare mutuncin aikin. "Sannan kuma su rungumi amfani da na'urori na fasahar zamani domin za su taimakawa inganta aikinsu," ya jaddada.
Shugaban na hukumar ICPC, Dakta Musa Adamu Aliyu ya yaba wa ƙoƙarin ƙungiyar lauyoyi reshen Ungogo jihar Kano bisa samar da mujallar da zai taimaka sosai wajen inganta aikin lauyoyin, tare da kira ga lauyoyin da yin amfani da dukkan abin da za su ƙaru.da shi don inganta aikinsu da ke mujallar.
Shi ma a nasa ɓangaren, shugaban ƙungiyar lauyoyi na ƙasa reshen Ungogo jihar Kano, Batista Ahmad Abubakar Gwadabe ya ce an samar da mujallar ne don faɗakar da al'umma, musamman lauyoyi irin aikace-aikacensu da abubuwa da ya kamata su sani tsakaninsu da waɗanda suke wakilta a kotuna ko a wasu harkokinsu.
Ya ce maƙasudin samar da mujallar
faɗakar da lauyoyi ya taimaka wajen ilmantar da al'umma, su ma lauyoyi a ƙara musu sani domin an saka wasu ƙasidu a ciki da muƙaloli da suka shafi harkar hada-hadar kuɗi da alaƙar lauya da wanda yake wakilta ko karewa.
"Sannan akwai muƙala da suka shafi doka da al'umma. Waɗannan sune kaɗan daga abubuwan da ke ƙunshe a mujallar," ya tabbatar.
Shugaban lauyoyi reshen Ungogo, Barista Ahmad Abubakar Gwadabe ya gode wa dukkan mahalarta taron da waɗanda suka ba da gudunmawa wajen ƙaddamar da mujallar da suka zo daga sassa na ciki da wajen jihar Kano.
Taron ya samu halartar lauyoyi da alƙalai da hukumomi daban-daban da 'yan kasuwa da dama da suka bayar da gagarumar gudunmawa a yayin ƙaddamar da mujallar.
No comments