Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa tana gudanar da manyan ayyukan raya ƙasa da darajarsu ta kai kusan Naira Biliyan 140 a f...
Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa tana gudanar da manyan ayyukan raya ƙasa da darajarsu ta kai kusan Naira Biliyan 140 a faɗin ƙananan hukumomi 14 na jihar, a wani shiri da aka bayyana a matsayin sabon babi na farfaɗowa da ci gaban Zamfara.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a Gusau, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Alhaji Mahmud Dantawasa, ya ce wasu daga cikin ayyukan sun kammala, yayin da sauran suke kan aiwatarwa — abin da ya nuna ƙudurin gwamnatin Gwamna Dauda Lawal na sake gina jihar cikin gaskiya da tsari.
Dantawasa ya bayyana cewa a kowace ƙaramar hukuma ana aiwatar da ayyuka da darajarsu ta haura Naira Biliyan 10, da suka haɗa da muhimman fannoni kamar kiwon lafiya, ilimi, hanyoyi, noma, samar da ruwa da bunƙasa kasuwanci.
“Wannan babban shiri ne da zai sake fasalin Zamfara, ya tabbatar da ci gaba mai ɗorewa tare da inganta rayuwar al’umma,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, a mafi yawan ƙananan hukumomin jihar ana gina sabbin hanyoyi na kilomita biyar a cikin birane, baya ga Gusau wadda ake gudanar da manyan ayyuka na musamman. Ya ce hakan zai rage cunkoso, ya haɗa al’umma, ya kuma farfaɗo da kasuwancin ƙauye da birane.
A fannin lafiya, gwamnati ta ƙaddamar da gina sabon babban asibiti a Nasarawa Burkullu a ƙaramar hukumar Bukkuyum, tare da sabunta cibiyoyin kiwon lafiya da dama a yankunan karkara, domin sauƙaƙa samun ingantaccen magani.
An kuma sanar da ci gaba da gyaran makarantu a dukkan ƙananan hukumomi, tare da samar da kujeru, littattafai, kayan koyo da horar da malamai domin tabbatar da ingantaccen ilimi ga yaran jihar.
Haka kuma, ana gina sabuwar kasuwa ta zamani a Nasarawa Burkullu, da ake sa ran za ta zama cibiyar bunƙasa sana'o’i da kasuwanci ga mazauna yankin. A bangaren ruwa da wutar lantarki kuwa, ana tono ruwan sha da kuma shimfiɗa sabbin hanyoyin rarraba wuta zuwa asibitoci, makarantun firamare da sakandare, da cibiyoyin gwamnati.
Dantawasa ya ce, an riga an kammala wasu daga ayyukan tare da ƙaddamar da su, yayin da sauran ke kan gaba, abin da ya tabbatar da cewa gwamnatin Lawal “ba ta tsaya kan magana kawai ba, tana aiki tare da sakamako a fili wanda jama'a ke iya gani da idonsu.”
“Wannan gwamnati ta tsayu kan gaskiya, amana, da samar da kyakkyawan sakamako ga al’umma. Ayyukan da ake gani su ne shaida,” inji Kwamishinan.
No comments