Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Jaridar NEW TELEGRAPH Ta Karrama Gwamna Lawal Da Lambar Yabo Ta Gwamna Mafi Nagarta Na Shekarar 2025

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya samu lambar yabo ta Gwamna Mafi Nagarta na Shekarar 2025 daga jaridar New Telegraph, sabo...

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya samu lambar yabo ta Gwamna Mafi Nagarta na Shekarar 2025 daga jaridar New Telegraph, saboda fitattun ayyukan sa na ci gaba a jihar.

Gwamnan ya karÉ“i wannan lambar yabo ne a ranar Juma’a, yayin bikin raba lambobin yabo da liyafar dare da jaridar ta shirya a babban É—akin taro na Lagos Oriental Hotel.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, an bayyana cewa jaridar ta girmama Gwamna Lawal ne saboda muhimman ayyukankawo sauyi da gwamnatinsa ke gudanarwa a muhimman sassa na jihar Zamfara.

Ya ce, “Jaridar New Telegraph ta naÉ—a Gwamna Dauda Lawal a matsayin Gwamna Mafi Nagarta na shekara ta 2025 saboda ayyukansa.
“Lambar yabo, wacce Hukumar Editoci ta Daily Telegraph Publishing Company ta bayar, ta gano yadda gwamnan da gwamnatinsa ke aiwatar da manyan sauye-sauye da ayyuka a fannoni kamar ilimi, gyaran birane, da samar da manyan abubuwan more rayuwa, domin inganta rayuwar al’umma da bunÆ™asa cigaba mai É—orewa a jihar.

“Jaridar ta kuma jero wasu dalilan karramawa, ciki har da Æ™oÆ™arin gwamnan na magance matsalar bashin ma’aikatan gwamnati da suka daÉ—e har tsawon shekaru 13 na dala miliyan 16, da kuma biyan kuÉ—in WAEC da NECO da aka bari fiye da shekaru uku, da sauran ayyuka masu muhimmanci.”
Yayin da yake karɓar lambar yabo, Gwamna Lawal ya gode wa hukumar gudanarwa da Hukumar Editoci ta Daily Telegraph kan ganin ya cancanci wannan girmamawa.
Ya ce, “Wannan karramawa tana Æ™ara min kwarin gwiwa da zai motsa ni da gwamnati na mu Æ™ara himma wajen aiwatar da Æ™arin ayyuka da tsare-tsare domin amfanin jama’a a jihar Zamfara.”

No comments