Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranci gwamnonin jihohi goma tare da shugabannin jam’iyya wajen tarbar Gwamnan ...
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranci gwamnonin jihohi goma tare da shugabannin jam’iyya wajen tarbar Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zuwa jam’iyyar APC.
An gudanar da wannan gagarumin taro ne a ranar Talata a filin kasuwanci na Trade Fair da ke Gusau, inda dubban magoya baya, ’yan Majalisar Dokoki, da mambobin Majalisar Zartarwa suka halarta domin shaida wannan lamari mai muhimmanci a siyasar jihar.
Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa Mataimakin Shugaban Ƙasar ya isa sabon filin jirgin saman Gusau na ƙasa da ƙasa, wanda aka kammala kwanan nan.
Daga cikin gwamnonin da suka halarci taron akwai Umar Namadi, Abba Kabir Yusuf, Uba Sani, Caleb Muftwang, Dapo Abiodun, Ahmad Aliyu, Ahmadu Fintiri, Dikko Radda, Muhammad Inuwa Yahaya, da Hope Uzodinma.
Haka kuma, manyan shugabanni sun haɗa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, tare da ministoci, jagororin jam’iyya da sauran manyan baƙi.
A jawabin sa, Mataimakin Shugaban Ƙasa ya bayyana cewa ƙarshen matsalar tsaro a Nijeriya yana gabatowa, yana mai cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na aiki tuƙuru domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin ƙasar.
Ya kuma yi addu’ar samun haɗin kai, ci gaba da zaman lafiya a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu, yana jaddada cewa gwamnati na ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Shettima ya ƙara da cewa, matsalolin tsaro a Zamfara da sauran jihohi za su samu mafita, inda ya nuna cewa shigar Gwamna Lawal cikin APC zai taimaka wajen cimma wannan buri. Ya kuma yi hasashen cewa jam’iyyun adawa ba za su samu karɓuwa sosai a Zamfara ba, saboda haɗin kan manyan ’yan siyasar jihar.
Shi ma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin APC, Gwamna Hope Uzodinma, ya bayyana cewa shigar Zamfara cikin APC babbar nasara ce, yana mai cewa gwamnonin jam’iyyar za su mara wa Gwamna Lawal baya domin ci gaban jihar.
A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya tabbatar da cewa zai tafiyar da mulkinsa bisa adalci da gaskiya, tare da ci gaba da hidimtawa al’ummar Zamfara yadda ya kamata.
Tsoffin gwamnonin jihar, ciki har da Abdulaziz Yari, Muhammad Bello Matawalle, da Mahmud Shinkafi, sun halarci taron, inda suka nuna goyon bayansu ga Gwamna Lawal tare da alƙawarin yin aiki tare da shi.
No comments