Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Dole Ne Dan Takarar Gwamna a Nasarawa ya zama Dan asalin Jiha

Inji Kungiyar Kabilun Jihar  Daga Zubairu Lawal  Wata ƙungiyar matasa a Jihar Nasarawa ta bayyana cewa duk da haƙƙin da gwamna k...


Inji Kungiyar Kabilun Jihar 

Daga Zubairu Lawal 

Wata ƙungiyar matasa a Jihar Nasarawa ta bayyana cewa duk da haƙƙin da gwamna ke da shi na bayyana wanda yake so a matsayin ɗan takarar da zai gajeshi.

 Dole ne a bi tsarin dimokuraɗiyya na gaskiya da adalci wajen zaɓen ɗan takarar gwamna a Jam'iyyar APC.

Da yake karanta kasidar gaban manema Labarai  Babban Kodineta na kungiyar Matasan  Kabilun Jihar, Kwamared Sales Dauda Yaleni, yace  Suna tunatar da Gwamna Abdullahi Sule, ya tuna  yadda aka bi ƙa’ida a lokacin da tsohon gwamna Umara Tanko Al-Makura ya  zabeshi a matsayin Wanda yake son ya gajeshi, ya Kuma yarda ya baiwa duk Yan Takara damar gudanar da Zaben fidda gwani.

Ƙungiyar ta nuna damuwa kan yadda aka bayyana Zaben ba tare da cikakkiyar tuntuba da haɗa kabilu daban-daban ba.

Tana mai kira da a gudanar da Zaben fidda gwani Mai cike da  adalci ga dukkan ‘yan takara a jam’iyyar APC domin a fitar da wanda jama’a suka amince da shi ta hanyar sahihin zaɓe.

Haka kuma, sun yi watsi da batun rabon kujeru (zoning), suna cewa ba doka ba ce a jihar, don haka ya kamata a bar jama’a su Zabe wanda suke so ba tare da wani matsin lamba ba. 

Sun kuma jaddada buƙatar ɗan takarar gwamna ya kasance ɗan asalin jihar, ba tare da la’akari da addini ba.

Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa ba za ta amince da tilasta tsayar da ɗan takarar da ba ɗan asalin jihar ba.

 tana mai cewa muradun cigaba  tana ga al’umma ne ba jam’iyya ba. 

A ƙarshe, ta yi kira ga jama’a da su guji kalamai masu tayar da hankali tare da jaddada aniyarta na kare makomar siyasar Jihar Nasarawa

No comments