Daga Ibrahim Muhammad Kano An bayyana zaɓin da Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi na Hon. Murtala Sule Garo a ma...
Daga Ibrahim Muhammad Kano
An bayyana zaɓin da Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi na Hon. Murtala Sule Garo a matsayin wanda zai zama mataimakinsa da cewa suna goyon bayan sa kashi 100 bisa 100.
Mai bai wa Gwamnan jihar Kano shawara na musamman kan wayar da kan mutane daga tushe, kuma tsohon shugaban ƙaramar hukumar Bunkure, Hon. Isma’ila Shehu Gurjiya, ne ya bayyana hakan.
Ya ce kowa ya san dacewar Murtala Sule Garo, domin an san ƙirƙinsa da iya mu’amalarsa.
Ya bayyana shi a matsayin jajirtaccen mutum wanda yake da ƙwarewa, kuma mutum ne mai karamci da girmama jama’a.
Ya yi nuni da cewa neman matsayin da ɗan yankinsu, Hon. Kabiru Alhasan Rurum, ya yi, dama nema ne. "Ba duk abin da mutum ya nema yake samu ba," in ji shi.
Ya ce a matsayinsu na ’yan yankinsa, da shi Allah ya ba wa wannan kujera, da kashi 100 bisa 100 za su yi murna su goyi bayansa. "Amma da yake Allah bai ƙaddara ba, suna yi masa fatan Allah ya kawo masa ci gaba mafi alheri," ya jaddada.
Hon. Gurjiya ya ce wannan kujera ta mataimakin Gwamnan Kano da aka bai wa Murtala Sule Garo, a fannin mu’amala da siyasa, kujera ce da za ta taimaka wa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wajen mu’amala da mutane da kuma samun nasara a zaɓuɓɓuka masu zuwa, saboda ya san zai bayar da gagarumar gudummawa wajen nasarar sake dawowar gwamnan.
Ya yi kira ga ’yan jam’iyya da su san cewa kowane al’amari rubutacce ne, kuma tsararre daga Ubangiji. "Don haka duk wani abu da ya zo, a ɗauke shi a matsayin ƙaddara daga Allah, domin Shi ne ya san alherin da yake cikinsa," a cewar sa.
Hon. Isma’ila Shehu Gurjiya ya yi kira ga ’yan jam’iyyarsu ta APC gaba ɗaya, da waɗanda suka zo cikin jam’iyyar da kuma waɗanda suka tarar, da su haɗa kai kamar yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf yake kira tare da nuna cewa Kano ce a gaba.
Ya ce su ɗauki Kano a matsayin abin fifiko domin dukansu ’yan Kano ne, kuma ba su da garin da ya wuce Kano.
"Saboda haka su haɗa kai su yi wa Kano aiki domin a gyara jihar, su ji daɗin zama, sannan ’ya’yansu da jikokinsu su zo su gaji alheri," ya ƙarƙare.
No comments