Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Gwamna Lawal Ya Amince Da Wani Shirin Gaggawa Don Ceto Ilimi A Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da wani shiri na musamman na kwanaki 120 domin magance manyan matsalolin da ke add...

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da wani shiri na musamman na kwanaki 120 domin magance manyan matsalolin da ke addabar tsarin ilimi a jihar.

Gwamnan ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar 65 a Gidan Gwamnati da ke Gusau a ranar Litinin, inda aka tattauna muhimman batutuwa da suka shafi bangarori daban-daban, ciki har da ilimi, lafiya da ayyukan raya ƙasa.

A cewar wata sanarwa, “A zaman Majalisar zartarwar na 65, gwamnatin ta amince da wani tsari na gaggawa da aka gina ne bisa bincike da nazarin da Ma’aikatar Ilimi da Hukumar Tabbatar da Ingancin Ilimi ta Jihar (EQAA) suka gudanar a baya.”
“Shirin na kwanaki 120, wanda muÆ™addashin Kwamishinan Ilimi, Abdulmalik Abubakar Gajam ya gabatar, ya Æ™unshi matakai da suka haÉ—a da tantance ma’aikata ta hanyar duba albashi, tsara taswirar makarantu da kuma duba yanayin gine-ginen makarantu.

Haka kuma, shirin ya tanadi aiwatar da sauye-sauye cikin gaggawa a bangarorin gudanarwa, gine-gine, fasahar zamani, horas da malamai da kuma kula da jin daÉ—in É—alibai, domin tabbatar da ingantaccen tsarin ilimi a jihar.

Bugu da Æ™ari, Majalisar ta amince da kafa wani kwamiti na haÉ—in gwiwa Æ™arÆ™ashin jagorancin Ma’aikatar Ilimi, Kimiyya da Fasaha, domin bincike da tantance dukkan gine-ginen da aka gina ba bisa Æ™a’ida ba a kusa da makarantu. An kuma ba kwamitin umarnin É—aukar matakin kwashe irin waÉ—annan gine-gine domin tabbatar da tsaro da tsaftar muhallin makarantu.

A wani muhimmin mataki, Majalisar ta amince da samar da dokar haɗaka guda ɗaya da za ta rufe dukkan matakan ilimi daga na yara ƙanana (ECCDE) zuwa manyan makarantu. An bayyana cewa za a gabatar da ƙudirin dokar ga Majalisar Dokokin Jihar domin amincewa da shi cikin gaggawa.
Haka kuma, Gwamna Lawal ya amince da sauya tsarin biyan albashi ga ma’aikatan da ba malamai ba, inda za a mayar da su zuwa wasu ma’aikatun gwamnati ko kuma kamfanoni masu zaman kansu, domin inganta tsarin aiki da rage cunkoso a bangaren ilimi.

Majalisar ta kuma amince da kafa Kwamitin Jagoranci na Jihar kan Dokar Ta-baci a Fannin Ilimi, tare da bai wa kwamitin damar kafa Kwamitin Kwararru (Technical Working Group) da kuma haɗa gwiwa da masu ruwa da tsaki kamar Ƙungiyar Malamai (NUT), UNICEF, Hukumar Ilimin Firamare ta Tarayya (UBEC), shugabannin gargajiya da na addini, masu makarantu masu zaman kansu da ƙungiyoyin farar hula.

Wannan mataki na nuna ƙudirin gwamnatin Zamfara na farfaɗo da bangaren ilimi, tare da tabbatar da cewa an magance matsalolin da suka daɗe suna tarnaƙi ga cigaban ilimi a jihar.

No comments