Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

HARIN TA'ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana matuƙar alhini da jimami kan mummunan harin da ’yan bindiga suka kai a wasu ƙauyu...

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana matuƙar alhini da jimami kan mummunan harin da ’yan bindiga suka kai a wasu ƙauyuka na Ƙaramar Hukumar Bukkuyum, wanda ya yi sanadin salwantar rayukan bayin Allah tare da jikkata wasu da dama.

Gwamnan ya bayyana harin da aka kai da dare a ƙauyukan Bunkasau, Yar Galma (Unguwar Zarumai) da kuma Dogon Daji (Unguwar Adabka) a matsayin mummunan aiki na tashin hankali da rashin tausayi, wanda aka aikata kan fararen hula marasa kariya.

Ya kuma miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa ’yan uwansu, yana mai nuna alhini da jimami tare da su a wannan lokaci na babban rashi da baƙin ciki.

A wani mataki na gaggawa, Gwamna Lawal ya umarci a tura wata babbar tawaga ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Gwamna domin kai saƙon jaje, tallafa wa iyalan da abin ya shafa, tare da tabbatar da cewa waɗanda suka jikkata sun samu kulawar lafiya cikin gaggawa.

Haka kuma, ya tabbatar wa al’ummar jihar Zamfara cewa gwamnatinsa za ta ƙara zage damtse wajen kare rayuka da dukiyoyi, tare da ɗaukar matakai masu ƙarfi domin dawo da zaman lafiya a dukkan sassan jihar.

No comments