Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Hukumar BON Ta Karrama Gwamnan Zamfara Da Lambar Yabo Ta Gwamnan Shekara A Fannin Ababen More Rayuwa

Hukumar kula da kafafen Watsa Labarai ta Nijeriya (BON), ta karrama Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, da lambar yabo ta “Gwamn...

Hukumar kula da kafafen Watsa Labarai ta Nijeriya (BON), ta karrama Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, da lambar yabo ta “Gwamnan Shekara a Fannin Ababen More Rayuwa,” sakamakon gagarumin ci gaban da gwamnatinsa ta samu musamman a shirin sabunta birane a faɗin jihar.

An miƙa wa gwamnan wannan babbar karramawa ne a yayin bugu na biyu na taron BON da aka gudanar a cibiyar taro ta NAF Conference Centre da ke birnin Abuja, inda manyan mutane daga sassa daban-daban suka halarta.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa ƙungiyar BON ta yaba da irin sauye-sauyen da ba a taɓa gani ba da gwamnatin Zamfara ta samu a fannin gine-gine da ababen more rayuwa, inda ta nuna cewa wannan karramawa ta wuce fannin watsa labarai kaɗai, tana nuna girmamawa ga nagartattun ayyuka a gwamnati.
Sanarwar ta ƙara da cewa, wasu fitattun ‘yan Nijeriya ma sun samu irin wannan karramawa a bikin lambar yabo ta Nigeria Broadcasting Awards na shekarar 2026. Daga cikinsu akwai Gwamnan Jihar Kuros Riba, Bassey Otu; Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani; Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na Ƙasa, Mohammed Idris; tare da wasu fitattun mutane kamar John Momoh, Shyngle Wigwe, Abubakar Jijiwa da kuma Sa'a Ibrahim.
Ƙungiyar BON, wadda aka kafa tun a shekarar 1973 domin kare muradun masu watsa labarai da inganta ƙa’idojin aikin jarida a Nijeriya, ta gudanar da tsauraran matakan tantancewa na watanni da dama kafin zaɓen waɗanda suka cancanci wannan karramawa.

Kwamitin zaɓen ya kasance ƙarƙashin jagorancin Danladi Bako, tsohon Darakta-Janar na Hukumar Kula da Watsa Labarai ta Ƙasa (NBC), tare da haɗin gwiwar ƙwararru daga National Broadcasting Commission da Advertising Regulatory Council of Nigeria.

Kwamitin ya bayyana cewa daga cikin dalilan da suka sa aka zaɓi Gwamna Lawal akwai irin gagarumin cigaban da ya samu a fannoni da dama, musamman yadda ya sauya fasalin birnin Gusau zuwa babban birni na zamani. Haka kuma, an ambaci manyan ayyuka da suka haɗa da gina filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa, inganta asibitocin gwamnati, da kuma ginawa da gyara tare da samar da kayan aiki a makarantu sama da 800 a dukkan ƙananan hukumomi 14 na jihar.

Sanarwar ta jaddada cewa wannan karramawa daga babbar ƙungiyar masu watsa labarai a Nijeriya za ta ƙara wa gwamnan ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da jajircewa wajen hidima da sake gina Jihar Zamfara domin al’umma.

No comments