Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

CI GABAN AL'UMMA: Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ta Jinjina Wa Gwamnan Zamfara

Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Amina Mohammed, ta bayyana cewa Jihar Zamfara yanzu ta zama mai sauƙin is...

Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Amina Mohammed, ta bayyana cewa Jihar Zamfara yanzu ta zama mai sauƙin isa ga masu zuba jari da abokan hulɗa, tare da jaddada cewa majalisar na shirye ta zama abokiyar hulɗa wajen bunƙasa jihar.

Amina Mohammed ta yi wannan bayani ne yayin wata ziyarar aiki da ta kai jihar Zamfara a ranar Alhamis, inda ta jagoranci tawagar manyan jami’an MDD domin duba halin da ake ciki a fannoni daban-daban.

Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce Mataimakiyar Babban Sakataren ta kai ziyarar gani da ido a Ƙaramar Hukumar Maru da wasu muhimman wurare, domin tantance ayyukan ci gaba da kuma fahimtar buƙatun al’umma kai tsaye.
Tawagar ta haɗa da wakilan manyan hukumomin MDD, ciki har da wakilin Shirin Raya Ƙasa na Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya, Elsie Attafuah; da shugabannin ƙasa na hukumomi irin su UNICEF, Hukumar Kula da Hijira ta Duniya, UNHCR, UNODC, UNAIDS da UNFPA.

A yayin gabatar da bayanai na bangarori daban-daban, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa gwamnatinsa na da tsare-tsare masu ƙarfi domin inganta ci gaba mai ɗorewa, da jure sauyin yanayi, da kuma haɓaka tattalin arziki mai haɗa kowa da kowa ta hanyar haɗin gwiwa.

Ya ƙara da cewa, Zamfara na kan wani muhimmin mataki na kawo sauyi, inda yawancin al’ummar jihar ke dogaro da noma, wanda ke zama ginshiƙin tattalin arzikinta.

A cewarsa, tsarin “Ajandar Ceto mai maki shida” wata dabara ce da aka tsara domin farfaɗo da jihar tare da tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.
A nata jawabin, Amina Mohammed ta yaba da yadda gwamnatin Zamfara ta gabatar da tsare-tsarenta cikin tsari, tana mai cewa hakan ya isa ya ja hankalin masu zuba jari da abokan hulɗa.

Ta ce, “Masu zuba jari na buƙatar yanayi mai kyau. Abin da ake buƙata yanzu shi ne zaman lafiya domin jawo hankalinsu. Abin da muka gani a yau ya nuna ƙwazon shugabanci da kuma hangen nesa, wanda shi ne abin da masu zuba jari ke nema.”
Ta kuma jaddada cewa, Zamfara na da ɗimbin damar ci gaba musamman a fannin ma’adinai, kasuwanci da noma, tare da nuna cewa akwai buƙatar haɗin kai daga kowane ɓangare domin cimma nasara.

“Na ga dama mai yawa, na ga kasuwa da buƙata, sannan na ga shugabanci da ke shirye ya haɗa kai da cibiyoyi da abokan hulɗa domin cimma nasara. Wannan aiki ba na gwamna kaɗai ba ne — kowa na da rawar da zai taka,” inji ta.
A ƙarshe, ta bayyana cewa MDD za ta ci gaba da tallafa wa jihar Zamfara, tana mai cewa, “Akwai fata mai yawa a nan, kuma muna shirye mu zama sahihin abokan hulɗa domin ganin an cimma burin ci gaba mai ɗorewa.”

No comments