Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

Yan majalisarJihar Nasarawa na APC Sun rokon sauran ya Takarar Gwamna da su amince da Wanda Gwamna Sule ya zabe.

Daga Zubairu Lawal  Yan Majalisan Sun roki sauran masu neman kujerar gwamna a APC da su hada kai su mara wa Wadada baya domin ya...


Daga Zubairu Lawal 

Yan Majalisan Sun roki sauran masu neman kujerar gwamna a APC da su hada kai su mara wa Wadada baya domin ya gaji Sule a 2027.

‘Yan majalisar jam’iyyar APC mai mulki a Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa sun amince da zabin Sanata Ahmed Aliyu Wadada da Gwamna Abdullahi Sule ya yi a matsayin wanda yake son ya gaje shi a 2027.

Dokta Danladi Jatau, Kakakin Majalisar, ya bayyana wannan goyon baya yayin da yake yi wa manema labarai bayani jim kadan bayan taron rukuni na 11 na ‘yan majalisar APC da aka gudanar a harabar majalisar jihar a Lafia a ranar Talata.

Kakakin majalisar, Hon. Danladi Jatau, ya ce ‘yan majalisar APC za su mara wa Sanata Wadada baya domin ya gaji Gwamna Sule a 2027.

An ruwaito cewa taron rukuni na 11 na ‘yan majalisar APC a Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ya gudana ne a ofishin Shugaban Masu Rinjaye Jama’a, inda Kakakin Majalisar Rt. Hon. Dr. Danladi Jatau da sauran ‘yan majalisar APC suka halarta.

Haka kuma, Kakakin ya bukaci al’ummar jihar da su goyi bayan Sanata Ahmed Aliyu Wadada, wanda Gwamna Abdullahi Sule ya zaba a matsayin dan takarar APC da yake so ya gaje shi a 2027.

Ya ce taron ya hada da tattauna hanyoyin karfafa hadin kai a tsakaninsu domin ci gaba da bunkasar jam’iyyar a jihar.

“Mun tattauna batutuwa da dama da suka shafi hadin kai, zaman lafiya da cigaban jam’iyya, da kuma goyon bayan da Gwamna Abdullahi Sule ya nuna wa Sanata Ahmed Aliyu Wadada a matsayin wanda yake son ya gaje shi.

Mu a matsayin ‘yan majalisar APC muna hade kai, kuma za mu ci gaba da kasancewa masu biyayya ga jam’iyya tare da bin shawarar Mai Girma Gwamna kan wanda ya zaba a matsayin magajinsa.

No comments