Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Breaking News:

latest

2027: APC Ta Amince Da Salon Mulkin Gwamnan Dauda Lawal, Ta Mara Masa Baya Ya Yi Tazarce

Jam’iyyar APC ta tantance tare da amincewa da Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, domin sake tsayawa takarar gwamna a zaɓen shek...

Jam’iyyar APC ta tantance tare da amincewa da Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, domin sake tsayawa takarar gwamna a zaɓen shekarar 2027.

Kwamitin tantance ’yan takarar na jam’iyyar mai mulki ƙarƙashin jagorancin Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ne ya tantance gwamnan a Abuja ranar Juma’a.

Tun a ranar Talata 5 ga watan Mayun 2026, wata tawaga ƙarƙashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Abubakar Nakwada, ta miƙa cikakkun fom ɗin nuna sha’awa da tsayawa takara na Gwamna Dauda Lawal ga kwamitin tantancewa na APC a Abuja.

Tun da farko dai masu ruwa da tsaki na APC a jihar Zamfara sun amince da Gwamna Dauda Lawal a matsayin ɗan takara guda tilo na jam’iyyar domin kujerar gwamna.

An cimma wannan matsaya ne a wani babban taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar ranar 25 ga watan Afrilun 2026 a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau, babban birnin Zamfara.

A yayin taron, shugabannin jam’iyyar sun kuma bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin sake neman wa’adi na biyu a babban zaɓen shekarar 2027.

Taron ya haɗa manyan jagororin APC daga sassa daban-daban na jihar, ciki har da tsoffin gwamnonin Zamfara guda huɗu; Ahmed Sani Yarima, Mahmuda Aliyu Shinkafi, Abdulaziz Yari da Bello Mohammed Matawalle.

Haka kuma, manyan jami’an gwamnati da aka zaɓa, dattawan jam’iyya, da wakilan matasa da mata daga faɗin jihar sun halarci taron.

Matakin amincewa da Gwamna Dauda Lawal na zuwa ne yayin da shirye-shiryen siyasa gabanin zaɓen 2027 ke ci gaba da ɗaukar zafi a sassa daban-daban na ƙasar nan.

No comments